
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a yankin ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, sun tsere daga gidajensu bayan hare-haren da aka zargi ‘yan bindiga da ke ƙarƙashin Bello Turji ne ke ƙaddamarwa a yankin.
Wannan al’amari ya sa da dama daga cikin mutanen yankin sun bar mazaunansu domin neman mafaka a wasu ƙauyuka mafi kusa da su.
A cewar masanin tsaro, Bakatsine mutanen suna cigaba ƙaura duk da cewa ana gudanar da azumin watan Ramadana yayin da ake cigaba da kashewa da sace mutane a yankin.
Ya ce, an ga yadda mutanen ke barin garin a yanayi na cincirindo da tattara kayayyakinsu cikin motoci domin ganin sun nesanta daga yankin.
A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, an ga mutane da dama na barin ƙauyen saboda fargabar fuskantar harin ‘yan bindiga.
Hakan na zuwa ne sakamakon munanan hare-hare da suka faru a yankin daga ‘yan bindigar da ake kyautata zaton yaran Bello Turji ne.
