Gidauniyar jin ƙai ta raba ɗinkunan Ƙaramar Sallah ga marayu a Dutsinma

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gidauniyar jin ƙai, da ke garin Dutsinma wadda ke ayyukan ta na tallafawa marayu, kiwon lafiya da kula da maƙabartu da sauransu ta raba tallafin ɗinkunan kayan sawa ga marayu maza da mata da ke a ƙarƙashin kulawar gidauniyar.

An gudanar da rabon tallafin ne domin bai wa waɗannan marayu kayan Sallah, ta yadda su ma za su gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki da walwala.

Daga cikin mahalarta taron akwai shugabannin gidauniyar da abokan hulɗar gidauniyar.

Gidauniyar ta ƙunshi irin su Abdul AK Foundation, Lado Development Foundation, ƙungiyar NUT reshen Dutsinma, ƙungiyar ɗalibai ta DUSA, HISBA Board da sauransu.

An gudanar da taron rabon tallafin ne a harabar babban ɗakin taro na ƙaramar hukumar Dutsinma.

Bayanin su na godiya, ɗaya daga cikin wanda suka amfana, sun nuna jin daɗin su da farin cikin su na samun wannan kulawa daga alumma ta hanyar Charity Foundation.

An kuma yi addu’ar Allah ya saka ma dukkan masu tallafawa da abubuwan alkhairi ga masu ƙaramin ƙarfi.

By ukarofi