Tinubu ya umarci a raba shinkafa ga Musulmi da Kiristoci yayin Ramadana da Lent

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya umarci Jakadun Shriin Sabunta Fata (Renewed Hope Ambassadors) da su raba shinkafa ga ‘yan Nijeriya a duk faɗin ƙasar domin tallafa wa masu azumin Ramadana da kuma Kiristoci da ke yin na Lent.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne Darakta Janar na shirin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 14 ga Maris, 2026.

A cewar Uzodimma, shirin rabon shinkafar na nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma nuna tausayi ga ‘yan ƙasa a wannan lokaci mai muhimmanci na ibada ga Musulmi da Kiristoci.

Ya ce, za a gudanar da rabon ne ta hanyar tsarin ƙungiyar na jihohi, ƙananan hukumomi da kuma gundumomi domin tabbatar da cewa iyalai da dama sun amfana da shirin.

Uzodimma ya ce irin wannan tallafi ya taba gudana a lokacin bukukuwan Kirsimeti na bara, inda aka raba shinkafa domin tallafa wa ‘yan Najeriya a lokacin bukukuwan.

Sanarwar ta janyo cece-kuce daga wasu masu nazarin siyasa, inda suke ganin matakin na iya zama wani mataki na fara kamfen gabanin zaɓen shekarar 2027.

Saidai, ba a bayyana yadda za a samu kuɗin rabon shinkafar ba ko adadin buhunan da za a raba ba da kuma inda za a samo su domin kaiwa ga al’ummar.

By Babaji