Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Yanzu haka wata tirka-tirka ta kin jinin gwamnatin jihar Kebbi ta kunno kai tare da mamaye kusan dukkan shafukaan sada zumunta a jihar Kebbi bayan fitar da wata takardar dakatar da wani Malamin firamare Malam Abduljalal Usman da hukumar ilmin bai ɗaya ta ƙaramar hukumar Dandi ta yi har na tsawon watanni uku tare da riƙe masa albashi bayan ya watsa wani bodiyon mudu ɗaya-ɗaya na shinkafa da dawa a matsayin nasa kaso a matsayinsa na malami.
A cewar Abuzaidu Yari, ba daidai ba ne a ce Gwamna ya san wannan lamari, kuma hukuncin dakatar da Malam Abduljalal ba a ɗauke shi bisa ƙa’ida ba.
Ya bayyana cewa a matsayinsa na wanda yake da haƙƙi, an riga an isar da wannan al’amari ga masu bincike domin duba shi sosai. Ya yi kira ga jama’a da su yi haƙuri saboda yana da tabbacin za a yi abin da ya dace ba da jimawa ba, kuma gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace.
Wannan sabon bayani ya ƙara tabbatar da cewa hukuncin dakatarwar malamin ba ya da goyon bayan Gwamnan Nasir Idris, sannan al’umma na da haƙƙin ganin adalci ya tabbata.
Masana da ‘yan uwa suna ganin cewa mataki irin wannan yana iya jawo cece-kuce, amma tuni an nuna cewa akwai hanyoyin shari’a da bincike domin tabbatar da gaskiya.
Sai dai daga baya kuma ofishin shugaban hukumar ilmi ta ƙaramar hukumar Dandi ta sake ftar da wata takardar soke dakatarwar don gudanar da bincike.
Yanzu haka dai ƙungiyoyin sa kai da kafafen sada zumunci na soshiyal media sun shiga wannan lamarin don ƙwatowa wannan malamin ‘yancinsa.
