Jami’an tsaro sun kai samame gidan Malami na Abuja sa’o’i bayan ziyarar Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An sake shiga fargaba a ranar Litinin yayin da jami’an tsaro suka kai samame a gidan tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewar al’amarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya kai masa ziyara a gidan nasa.

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, an ga yadda Malami yake ƙalubalantar jami’an tsaron kan sahihancin umarnin da suka zo da shi, yana mai cewa batun na gaban kotu kuma bai kamata a ɗauki wani mataki ba ba tare da umarni daga gare ta ba.

Saidai, jami’an sun ce suna da izinin yin alama a kadarorin da ke ƙarƙashin bincike a hukumance, don haka akan ƙa’ida suke.

Malami ya musanta zarge-zargen da ake masa, inda ya ce zai kare kansa a gaban kotu, tare da zargin cewa ana masa rashin adalci akan al’amarin.

Tsohon Antoni-Janar na Ƙasar na fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi safarar kuɗi tare da wasu ‘yan uwansa, yayin da shari’ar ke cigaba da gudana a kotu, wadda aka faro tun ƙarshen shekarar da ta gabata.

By Babaji