Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta jaddada cewa za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a Jihar Zamfara cikin lokaci.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima ya bayyana hakan a lokacin bikin karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar APC da ya gudana a Zamfara Trade fair complex a Gusau babban birnin jihar yau Talata.

Shatima ya bayyana cewar komawar Gwamna Dauda Lawal APC wani gagarumin cigaba ne, yana mai jaddada cewa gwamnatin tarayya za tayi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Zamfara don kawo ƙarshen yan ta’adda da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

A cewar sa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya damu da halin da alummar jihar da sauran jihohin da ke fama da matsalar tsaro, yana mai nuni da cewa, gwamnatin Tarayya za tayi iya ƙoƙarin ta don kakkaɓe dukkanin masu ayyukan ta’addanci a jihar da sauran jihohin da ke fama da matsalar da ikon Allah.

“Ina so inyi amfani da wannan damar in jinjinawa manya manyan ‘yan siyasar Jihar Zamfara musamman yayan jam’iyyar APC bisa karɓar Gwamna Dauda Lawal tare da ƙoƙarin ganin an samu haɗin Kai a tsakanin jagororin jam’iyyar da magoya bayan ta”. Shatima yace

“Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zata yi iya ƙoƙarin ta tare da haɗin gwiwa da gwamnatin Zamfara da jihohin Arewa maso Yamma da ke fuskantar natsalar tsaro don kawo ƙarshen natsalar cikin ƙanƙanin lokacin”. A cewar Kashim Shatima

Shatima yayi Kira ga mambobin jam’iyyar APC da al’ummar Zamfara su zauna lafiya tare da bai wa Shugaba Tinubu goyon bayan da ya dace a zaɓen da ke tafe a shekarar 2027.

By ukarofi