Kotu ta gano kurakurai a ƙarar El-Rufai ta zargin take haƙƙinsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta nuna kura-kurai a cikin ƙarar take haƙƙin ɗan Adam da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar kan wasu hukumomi da jami’an gwamnati.

Alƙali Joyce Abdulmalik ta bayyana hakan ne a zaman kotu na ranar Laraba, inda ta soki tsarin da aka bi wajen gabatar da ƙarar, musamman yadda ba a kai wa ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara sammaci ba.

Lauyan El-Rufai, Ugochukwu Nnakwu, ya shaida wa kotu cewa har zuwa lokacin ba a samu damar isar da sammaci ga babban alƙalin kotun majistare da aka saka a cikin ƙarar a matsayin wanda ake ƙara na biyu ba.

Ya ƙara da cewa sun shigar da buƙatar a ba su damar amfani da wata hanya ta musamman domin kai masa sammaci.

Sai dai alƙalin ta katse shi, tana mai jaddada cewa dole ne a fayyace sunan takamaiman alƙalin majistare a cikin takardar buƙatar. Ta bayyana cewa rashin yin hakan kuskure ne na shari’a da ya kamata a gyara.

Bayan amincewa da kuskuren, lauyan ya roƙi kotu ta ba su lokaci domin gyara takardun ƙarar yadda ya kamata. Lauyoyin sauran ɓangarorin da ake ƙara, ciki har da na Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Sufeto Janar na ’Yan Sanda, da kuma Babban Lauyan Tarayya, ba su nuna adawa da wannan buƙata ba.

Daga nan ne kotu ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga Maris domin ci gaba da sauraron ƙarar, tare da umartar a sake fitar da takardar sammaci ga wanda ake ƙara na biyu.

A cikin ƙarar da ya shigar, El-Rufai na neman kotu ta yanke hukunci cewa farmakin da jami’an ICPC da ’yan sanda suka kai gidansa da ke unguwar Asokoro a Abuja, a ranar 19 ga Fabrairu, ya saɓa wa kundin tsarin mulki tare da take masa haƙƙoƙinsa na mutunci, ’yanci, sauraron shari’a cikin adalci da kuma sirri.

Har ila yau, ya buƙaci kotu ta haramta amfani da duk wata hujja ko kayan da aka kwaso daga gidansa yayin binciken, yana mai cewa an samo su ne ta hanyar da ta saɓa wa doka. Ya kuma nemi a mayar masa da dukkan kayayyakin da aka ɗauka, tare da cikakken bayani a kansu.

Bugu da ƙari, tsohon gwamnan ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan ɗaya a matsayin diyya kan abin da ya kira take masa haƙƙi.

Sai dai a martanin da ICPC ta gabatar, ta bayyana cewa ta gudanar da binciken ne bisa ƙorafi da ta samu, tare da samun sahalewar kotu ta hanyar takardar izinin bincike kafin kai samamen.

Ta ce an gudanar da aikin cikin doka, kuma matar El-Rufai, Hadiza, da ɗansa Mohammed sun shaida abin da ya faru.

Haka kuma, rundunar ’yan sanda ta ƙara da cewa tana da cikakken ikon doka wajen bincike da kama masu laifi, tare da jaddada cewa duk abin da aka yi ya bi ƙa’ida.

By ukarofi