Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja ta sallami tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah, daga dukkanin tuhume-tuhumen damfara da ake yi mata, bayan an cimma yarjejeniyar sasanci tsakanin ɓangarorin da ke shari’ar.
Mai shari’a, Hamza Muazu, ne ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis a reshen kotun da ke Maitama, bayan da Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya janye ƙarar da ake yi wa tsohuwar ministar da kuma tsohuwar mataimakiyarta, Gloria Odita.
Lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo (SAN), ya bayyana wa kotu cewa an cimma matsaya ta sasanci, wato plea bargain, lamarin da ya sa aka sauya tuhumar da ake yi a baya.
A sabuwar tuhumar, an cire sunan Stella Oduah da mataimakiyarta daga cikin waɗanda ake tuhuma, inda aka bar kamfanoni biyu kaɗai masu alaƙa da ita — Sobora International Limited da Global Offshore and Marine Limited — a matsayin waɗanda ake tuhuma.
Kotun ta ji cewa kamfanin Sobora International Limited na da laifin mallakar kuɗi har Naira miliyan 838 ba bisa ƙa’ida ba, yayin da Global Offshore and Marine Limited ake zargi da riƙe Naira biliyan 1.629 ta haramtacciyar hanya.
Lokacin da aka koma zaman kotu, Stella Oduah ta bayyana a matsayin wakiliyar kamfanonin, inda ta amsa laifin a madadinsu. Bayan haka, lauyan gwamnati ya roƙi kotu da ta yanke hukunci kan kamfanonin, tare da umartar rufe su baki ɗaya da kuma ƙwace dukkanin kuɗaɗen da aka gano a bincike.
Daga cikin buƙatun da aka gabatar, an roƙi kotu ta amince da ƙwace Naira biliyan 1.2 da aka biya a matsayin diyya, tare da wani ƙarin Naira miliyan 780 da jami’an bincike suka gano, a mika su ga Gwamnatin Tarayya. Lauyan kamfanonin, Onyechi Ikpeazu (SAN), bai yi adawa da wannan buƙata ba.
A hukuncinsa, Mai shari’a Muazu ya same kamfanonin da laifi bisa ga amincewar da suka yi, inda ya umarci a rufe su gaba ɗaya. Haka kuma, ya amince da ƙwace dukkanin kuɗaɗen da aka ambata, domin miƙa su ga Gwamnatin Tarayya.
Daga bisani, kotun ta soke tsohuwar tuhumar da aka shigar ranar 13 ga Oktoba, 2025, wadda ta haɗa da Stella Oduah da mataimakiyarta, tare da sallamar su daga shari’ar gaba ɗaya.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen wata shari’a mai ɗaukar hankali a ƙasar, wadda ta shafi tsohuwar mamba a majalisar ministoci. Duk da cewa kamfanonin da ke da alaƙa da ita an same su da laifi kuma an umarci a rufe su, ita kanta Stella Oduah ta samu ’yanci daga shari’ar, lamarin da ya zama wani muhimmin juyin hali a wannan doguwar fafatawa ta shari’a.
