Kotu ta ba da umarnin kama shugaban PDP, Tanimu Turaki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayar da umarnin kama tsohon shugaban jam’iyyar PDP na tsagi ɗaya, Tanimu Turaki, bayan ya gaza halartar kotu domin amsa tuhumar da ake yi masa.

Alƙalin kotun, Peter Kekemeke, ne ya bayar da wannan umarni, inda ya ce dole ne a tilasta wa Turaki ya bayyana a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Rahotanni sun nuna cewa ana tuhumar Turaki da laifin bayar da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda, tuhuma da aka shigar a ƙarƙashin jagorancin Kayode Egbetokun, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya.

A zaman kotun na ranar, lauya mai gabatar da ƙara, Usman Rabiu, ya bayyana cewa an tanadi zaman ne domin wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa ko ya musanta, amma bai bayyana ba duk da cewa an aika masa da sammaci da takardar tuhuma.

Lauyan ya kuma jingina da sashe na 396(2) na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015, inda ya roƙi kotu ta bayar da umarnin kama wanda ake tuhuma domin tabbatar da halartarsa.

Sai dai lauyan ɓangaren kariya, Abdulaziz Ibrahim, ya buƙaci kotu ta ba shi ƙarin lokaci domin gabatar da rubutattun hujjoji, yana mai cewa sun shigar da ƙorafi kan a soke tuhumar gaba ɗaya.

A yayin da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Peter Kekemeke ya bayyana cewa duk da cewa Turaki ya san da ranar shari’a kuma an sanar da shi, rashin zuwansa ba tare da wata hujja ba ya saɓa wa doka.

Ya ƙara da cewa, dokar ta tanadi cewa idan wanda ake tuhuma ya ƙi bayyana a kotu duk da sanin ana nemansa, to ya dace kotu ta bayar da umarnin kama shi domin tilasta masa bayyana.

Haka kuma kotun ta ce buƙatar da ɓangaren kariya ya shigar na soke tuhumar ba za a saurare ta ba sai bayan an karɓi amsar wanda ake tuhuma.

Daga ƙarshe, kotun ta bayar da umarnin kama Turaki tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Afrilu domin a gurfanar da shi.

By ukarofi