
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan Nijeriya Samson Adamu kuma shugaban hukumar gudanarwar ƙwallon ƙafar Nijeriya ya zama sabon Babban Sakataren Hukumar Kula da Ƙwallon ta Afirka, CAF.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon sakatare, Veron Mosengo-Omba daga Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Kongo Democratic ya yi murabus daga muƙamin.
Wannan na nuna ƙaruwar tasirin Nijeriya a harkar ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Afirka.
Gabanin naɗin nasa, Adamu shi ne Daraktan gasa da taruka na CAF.
Kwamitin zartarwar CAF ne ya bayar da sunan ɗan Nijeriyar busa la’akari da gogewarsa a fannin ƙwallon ƙafa a wani zama da ya gudanar a Kairo, babban birnin Misra.
