‘Yan bindiga sun halaka mutane uku da ƙone gidaje da rumbuna a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari ƙauyen Ɗangoro da ke gundumar Nahuche a Ƙaramar Hukumar Bungudu, inda suka kashe mutane uku tare da lalata gidaje da wasu kadarori.

Al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Asabar wayewar Lahadi.

‘Yan bindigar sun shigo ƙauyen ne dauke da bindigogi ƙirar AK-47, inda suka riƙa harbe-harbe tare da cinna wa gidaje da rumbunan abinci wuta.

Jami’an ‘yan sanda da haɗin gwiwar dakarun sa-kai (Vigilante) sun isa wurin cikin sauri, inda aka gwabza faɗa da ‘yan bindigar har sai da aka kore su zuwa cikin daji da raunukan harbi a jikinsu.

Mutane biyar sun samu raunukan harbin bindiga, yayin da wasu huɗu suka samu raunukan ƙonewa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya bayyana cewa an garzaya da dukkan waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Gusau domin karɓar magani.

By Babaji