Yadda sabon rikicin Jos ya dawo ɗanye

Spread the love

*IGP Disu ya ziyarci Filato 

*’Yan majalisun tarayya daga Filato sun kai ziyarar jaje

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, a Jos 

Al’ummar garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, sun sake shiga wani sabon ruɗani da firgici sakamakon ɓarkewar wani sabon rikici, wanda ya samo asali daga harin ’yan bindiga da aka kai wani yanki na unguwar Rukuba da ake kira Gari Ya Waye, inda ake cin kasuwar dare da mashaya. An kai wannan hari ne ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026, da daddare da misalin ƙarfe 8:00 na dare, yayin da yankin ke tsaka da hada-hada, kamar yadda aka saba.

Wannan hari na ‘yan bindiga da aka ce sun far wa wajen ne akan babura, ya haifar da asarar rayuka kimanin 28, kodayake a rahoton farko Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Filato ta sanar da cewa, mutane 14 ne suka rasa rayukansu, ciki har da mata guda biyu. 

Bincike ya nuna cewa, daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a wannan harin, akwai Musulmi da harin ya rutsa da su suna gudanar da kasuwancinsu a wajen. ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da ke wakiltar al’ummar Musulmin jihar, ta bakin sakatarenta, Dr Salim Musa Umar, ta bayyana cewa, an kashe Musulmi 4 yayin da ake neman wasu mutum 10 da ba a gan su ba tun bayan harin da aka kai na daren ranar Lahadi, yayin da daga bisani aka gano wasu mutane biyu Musulmi da suka samu jikkata, suna jinya a Babban Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Jos (JUTH).

Daga bayanan da wakilin Blueprint Manhaja ya tattara mana, ya gano cewa, bayan afkuwar wannan mummunan hari, matasan yankin unguwar Rukuba, wacce unguwa ce ta Kirista, sun fusata sosai, inda suka bazu akan babban titin zagaye zuwa Bauchi, wanda a turance ake kira da Bauchi Ring Road, a dalilin haka sun riƙa tare masu wucewa da ake ganin suna da alamun Musulunci, suka riƙa bugun su, har ma da ƙona wasu gawarwarki daga cikinsu. Akwai hotunan bidiyo na irin mummunan kisan da suka riƙa yi cikin fushi a cikin daren da abin ya faru, wanda aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Har wa yau, a cikin daren ne wani Bature ɗan asalin ƙasar Amurka, wanda aka bayyana sunansa da Aleɗ Barbir ya fitar da wani hoton bidiyo a shafinsa na Facebook, wanda ya ɗauka a gaban wani babur ɗin Keke Napep na Musulmi da aka sanya wa wuta, yana ƙalubalantar Shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harin da aka kai tare da alaƙanta abin da ya faru da kisan ƙare dangi da ake zargin ana yi wa Kirista a Nijeriya, duk da cewa hoton bidiyon na Musulmi ne aka farwa.

Wannan bidiyo da ya fitar da wasu bayanai makamantan nasa da wasu daga cikin shugabannin matasan Kirista suka riƙa yi, wanda aka riƙa yaɗawa a zaurukan sada zumunta, sun ƙara tunzura jama’a da hasala mabiya addinin Kirista a faɗin jihar. 

Akwai bayanai masu karo da juna daga waɗanda abin ya faru akan idanunsu, inda wasu ke cewa, wasu mutane ne akan babura suka far wa unguwar sanye da kayan sojoji sun rufe fuskokinsu suka buɗe wuta kan mutane. Yayin da wasu ke cewa, maharan sun je ne a wata farar mota, sannan suka riƙa buɗe wuta akan mutane. Sannan kasancewar unguwar Rukuba waje ne da ya ƙunshi mutane masu tu’ammuli da kayan maye da miyagun ƙwayoyi, suna yawan samun ziyarar jami’an Hukumar Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta NDLEA, don haka lokacin da aka fara jin harbe-harbe, jama’a da dama sun yi zaton ko an je farautar ’yan shaye-shaye ne.

Fargabar halin da za a wayi gari da shi a garin Jos a safiyar Litinin ya sa gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ta hannun Kwamishinan Yaɗa Labarai ta Jihar Filato, Joyce Ramnap, ya sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon awoyi 48 a faɗin ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, domin hana watsuwar rikicin, kamar yadda aka saba gani a rikice-rikicen da suka faru na baya.

Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang, wanda lokacin da lamarin ya faru ba ya gari ya tafi wata ziyarar aiki Babban Birnin Tarayya Abuja, cikin gaggawa ya yanke abin da yake yi ya dawo gida Jos, domin duba halin da ake ciki. Cikin rakiyar jami’an tsaro tawagar gwamnan ta isa unguwar Rukuba, domin jajenta wa jama’ar yankin kan abin da ya faru. An ga gwamnan cikin motar sulke ta ’yan sanda yana magana da dafifin jama’ar da suka fito, don nuna alhini da ɓacin rai game da rashin ’yan uwa da suka yi.

Kodayake matasan unguwar sun nuna fusata da nuna rashin jin daɗin yadda suka ga gwamnan ya tsaya a saman motar ’yan sandan ba tare da ya sauka ba, har sai da kwamishinan ’yan sanda na jihar, Bassey Ewah da wasu manyan jami’an ‘yan sanda suka bai wa gwamnan kariya sannan ya sauka ya gana da wakilan al’ummar yankin. Ya bayyana damuwa da alhininsa kan abin da ya faru tare da alƙawarin gudanar da bincike, don gano waɗanda suka kitsa wannan kashe-kashe. Sannan ya yi alƙawarin gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin jana’izar waɗanda aka kashe tare da biyan diyya.

Su ma matasan yankin sun nemi lallai gwamnati ta sa a kamo wani matashi da ya taɓa yin wani bidiyo a zaurukan sada zumunta yana barazanar cewa, bayan sallah za su kai hari Jos, don ɗaukar fansar abubuwan da suka faru yayin kisan gillar da aka yi wa wasu ’yan kasuwa matafiya a hanyar Barikin Ladi. A cewarsu, harin da aka kai na da nasaba da wancan bidiyo da aka fitar, wanda a zargin da suke yi Musulmi ne suka shirya kai musu harin, domin cimma wani muradinsu, buƙatar da Gwamnan ya amince za a yi a wani ɓangare na gano waɗanda ke da hannu wajen kai wannan hari.

Reshen ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Musulmi ta MURIC da ke Jihar Filato ya zargi Gwamna Mutfwang da nuna wariya da bambanci ga al’ummar Musulmi, saboda a yayin da gwamnan ya ziyarci ɓangaren unguwar Rukuba, domin yi musu jajen abin da ya faru, bai ziyarci ɓangaren Musulmi ba, waɗanda su ma sun rasa rayukan mutanensu, kuma ko a cikin jawabin da ya gabatar ga al’ummar jihar bai ambaci Musulmi ba.

ƙungiyar, ta bakin shugabanta, Abubakar Sadiƙ Yusuf ta nuna rashin gamsuwa da yadda Gwamnan yake tafiyar da al’amuran da suka shafi tsaro da zaman lafiya a matsayinsa na jagoran al’umma bakiɗaya. 

Sannan a ranar Litinin ɗin Shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, John Kyoroh Christopher ya kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a ƙaramar hukumar, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi a taƙaita watsuwar rikicin, kuma a ɗauki matakan tsare rayuka da dukiyoyin jama’a a kasuwanni da kan hanyoyi, saboda ɓatagari da za su yi amfani da halin da ake ciki wajen haifar da ɓarna da sace-sace.

A ganawarsa da wakilin Manhaja Blueprint, Mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Kabiru Muhammad Sani Garkuwa, ya yi kira ga matasa da su kai zuciya nesa kuma su yi haƙuri kan abubuwan da suka faru, domin bai wa jami’an tsaro damar yin bincike da nufin gano waɗanda suka shirya wannan hari, don a hukunta su bisa tanadin doka.

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, ta bakin Kakakin Rundunar ‘‘Yan Sanda ta ƙasa, DCP Anthony Okon Placid ya bayar da umarnin kai ƙarin jami’an tsaro zuwa Jihar Filato, domin taimaka wa wajen samar da tsaro da dawo da kwanciyar hankali a cikin garin Jos. Ta kuma roƙi jama’ar jihar su bai wa jami’an ’yan sandan haɗin kai da taimaka musu da muhimman bayanai da za su taimaka musu a aikin da za su gudanar.

A wata sanarwa da reshen ƙungiyar Kiristan Nijeriya ta CAN dake Jihar Filato ya fitar ta hannun shugaban ƙungiyar na jihar, Rabaran Dunka Joseph Gomwalk da Sakataren ƙungiyar Pasto Julius, Simon Arabo, ya yi Allah wadai da wannan mummunan hari da aka kai wa mazauna yankin unguwar Rukuba a daren ranar da suka gudanar da ibadar Palm Sunday mako guda kafin gudanar da bikin Easter. A cewar ƙungiyar wannan hari ne da aka kai kan Kirista, domin addininsu. Kuma ta nemi jami’an tsaro da gwamnati su gudanar da cikakken bincike domin gano masu aikata wannan ta’addanci, don a hukunta su, a kuma kare wa jama’a haƙƙinsu.

Haka kuma haɗin gwiwar ƙungiyoyin Matasan Musulmi na NACOMYO da na Kirista YOWICAN ta hannun shugaban ƙungiyar ɓangaren Musulmi, Barista Yahaya Ali Ali da shugaban ɓangaren Kirista, Barista Penmak Mark Lere, sun ja hankalin matasa su guji ɗaukar doka a hannu, su taimakawa jami’an tsaro wajen tsare unguwanninsu da samar da zaman lafiya, don jama’a su koma cikin harkokinsu ba tare da tsangwama ko fargabar komai ba.

Sai dai duk da waɗannan kiraye-kiraye a ranar Laraba, 1 ga Afrilu, 2026, bayan da Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da sassauta lokacin dokar hana zirga-zirga, ya koma daga karfe 7:00 na safe zuwa 3:00 na yamma, ana buɗe gari bayan jama’a sun fito domin gudanar da harkokin su da shiga kasuwanni da nufin yin cefane, sai aka ga wasu matasan Kirista daga yankin unguwar Rukuba sun fito bakin hanya kan iyakarsu da ɓangaren Musulmi na Nasarawa Gwong riƙe da makamai ƙirar gida da duwatsu suna jifan masu wucewa da waɗanda ke bakin gidajensu a ɗaya ɓangaren. Wannan ya hasala matasa a ɓangaren Musulmi suka fara mayar da martani aka riƙa jefe-jefe, ana yi wa juna ɓarna. A sakamakon haka an jikkata mutane da dama waɗanda harbin bindigar boris da duwatsu ya shafa, yayin da ake zargin wasu harsashi ne mai rai ya jikkata su. 

Wannan tarzoma ita ce ta watsu har zuwa wasu sassan garin Jos, inda a unguwannin da Musulmi suka fi yawa, ake kai farmaki kan Kirista. Haka su ma Kirista a nasu unguwannin suka riƙa kai farmaki ga Musulmi masu wucewa ko kasuwanci. Kamar abin da ya faru a Titin Bauchi, Farar Gada, Gada Biyu da Dutse Uku. Kawo lokacin haɗa wannan rahoto dai babu wani sahihin rahoto game da adadin mutanen da suka rasu ko suke jinya a asibiti.

A wani taron manema labarai da kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Filato ya kira ranar Laraba da yamma, bayan tsagaitawar rikicin, ya sanar da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu wajen tayar da wannan tarzoma, ciki har da wani da ake zargi da yin sojan gona, mai suna Yakubu Abdullahi mai shekaru 26, wanda aka kama shi sanye da rigar soja da kuma katin shaidar karatu a makarantar sojoji ta Nigeria Military School, wanda shi ma ake zargin na bogi ne. Sannan an kama wani mai suna Mathew Musa mai shekaru 27, wanda aka kama da wasu bindigogi guda biyu ƙirar gida, inda ake zargin an yi amfani da su wajen kashe-kashen  da aka yi.

Biyo bayan yadda Musulmi da Kirista ke jifan juna da zarge-zarge da kalamai na tunzura juna a kafafen sada zumunta, ciki har ma da wani da ya yi barazanar cewa, wata ƙungiyar Kirista masu ɗauke da makamai za ta kai hari kan masallatan Juma’a da wuraren zaman Musulmi, domin ramuwar gayya. Hakan ya sa ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam ta fitar da wata sanarwa ga limamai da masu unguwanni a dukkan ƙananan hukumomin Jihar Filato 17 su tsaurara matakan tsaro a wurarensu na ibada da unguwanninsu tare da sa ido kan duk wani abu da ba su amince da shi ba a kewayensu. Sannan a gudanar da addu’o’in zaman lafiya a ko’ina a faɗin jihar tare da roƙon Allah Ya tona asirin masu neman tayar da fitina a jihar. 

A wani ɓangare na bayyana damuwa da yaɗuwar wannan rikici shugaban ƙaramar Hukumar Mangu, Emmanuel Bala Mwolpun, ya kafa dokar hana zirga-zirga a yankin, biyo bayan ƙaruwar fargaba da tsoron ɓarkewar rikici a ƙaramar hukumar. Idan za a iya tunawa ita ma ƙaramar Hukumar Mangu na daga cikin ƙananan hukumomin Jihar Filato da ke fama da matsalar rikice-rikicen ƙabilanci da na addini.

Sakamakon wannan rikici, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya karkatar da ziyarar da zai kai jihohi guda huɗu, inda ya fara da jihar ta Filato, don duba halin da ake ciki.

Bugu da ƙari, Babban sufeton ’yan sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu ya jajenta wa gwamnati da al’ummar Filato bisa harin ta’addanci da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wasu bayin Allah yayin da suke gudanar da kasuwancinsu a kasuwar Gari Ya Waye dake unguwar Rukuba a cikin garin Jos a daren Lahadin da ta gabata, 29 ga Maris, 2026.

Babban Sufeton ya bayyana haka ne a yayin da ya ziyarci Jihar Filato, domin nazarin halin da tsaron jihar ke ciki, bayan amincewa da ƙarin jami’an ’yan sanda na musamman zuwa Jos, inda aka samu rashin zaman lafiya. 

IGP Disu ya tabbatar wa da jama’ar Filato cewa, rundunar ’yan sanda za ta yi duk abin da ya kamata, don kawo ƙarshen asarar rayuwa da ake yawan samu a jihar. Ya yin da ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, kuma su yi biyayya ga doka, don sauƙaƙa ayyukan da ’yan sandan suke gudanarwa. 

A jawabinsa na maraba, Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya yabawa Babban Sufeton bisa ƙarin jami’an ’yan sanda da ya tura jihar, domin taimaka wa waɗanda ake da su a ƙasa, don inganta aikin samar da tsaro da kiyaye doka da oda. Ya kuma yaba wa Kwamishinan ’yan sanda na jihar Bassey Ewah, da sauran rundunonin tsaro bisa rawar ganin da suka taka wajen shawo kan matsalar tsaro da aka fuskanta a unguwar Rukuba, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki dukkan matakan da suka kamata don ganin an hukunta masu hannu a wannan hari.

Gwamnan ya ce, kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Filato ya yi ƙoƙari sosai wajen ganin an daƙile bazuwar rikicin zuwa sassan jihar. Ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa ɓangaren tattara bayanan sirri, don magance sake faruwar makamancin haka.

A wani ci gaban ma, zaɓaɓɓun ’yan majalisar ƙasa da waɗanda aka yi wa naɗe-naɗen muƙaman siyasa daga Jihar Filato sun kai ziyarar jaje da ta’aziyya game da asarar rayuka da aka yi, sakamakon harin ‘yanbindiga a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. 

Tawagar ’yan majalisar da suka haɗa da sanatoci, ‘yan majalisar wakilai, ministoci, da tsofaffin gwamnoni, sun je ne ƙarƙashin jagorancin Sanata Simon Baƙo Lalong mai wakiltar Shiyyar Filato ta Kudu, ya kuma shaidawa Gwamnan jihar Caleb Manasseh Mutfwang cewa sun kai ziyarar ne domin jajentawa Gwamnati da al’ummar Filato bisa mummunan harin da aka kai Anguwar Rukuba a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, wanda ya jawo asarar rayuka da dama.

Sun ce za su cigaba da goyon bayan gwamnatin Gwamna Caleb Mutfwang a kowanne yanayi, domin ta samu nasara akan maƙiyan Filato, ba tare da nuna bambancin addini ko siyasa ba.

Sanata Lalng ya ce, duk ‘yan siyasar jihar na tare da jama’ar Filato a wannan hali da ake ciki na jimami da alhini da ake ciki.

A jawabinsa Gwamna Caleb Mutfwang ya yi wa ‘yan siyasar godiya bisa wannan goyon baya da suka nuna masa da al’ummar Jihar Filato, don haka ya ce, jama’ar Filato za su cigaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Ya kuma bayyana musu cewa, daga cikin matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka har da tabbatar da aiki da dokar hana aikin achaɓa a cikin garin Jos bakiɗaya. 

Ya kuma tabbatar musu da cewa jami’an tsaro na nan suna gudanar da bincike, domin gano masu hannu a wannan ta’addanci da aka kai wa al’ummar jihar.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto gari Jos ya kasance cikin lumana babu wata hayaniya, sai dai babu walwala sosai kuma ana cikin rashin tabbas, lamarin da ya haifar da dawowar saɓanin zamantakewa ɗanye.

By ukarofi