Gwamnatin Katsina ta yi Allah-wadai da kisan mutum biyu a Ɗanja

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi kakkausar suka tare da Allah-wadai da mummunan kisan da ya faru a ƙauyen Kokami, gundumar Yakaji ‘A’, a ƙaramar hukumar Danja ta jihar.

Lamarin wanda ya faru ya samo asali ne daga saɓani tsakanin mutane biyu Ibrahim Khalil Auwal da Mr Joe (wanda aka fi sani da K.C. Jones) kan sayen garin rogo da ruwan leda a shagon K.C. Jones.

Kamar yadda kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya sanar , mutanen biyu da gardama ya haɗa su daga baya ya rikiɗe zuwa tashin hankali.

Kwamishinan ya ce an ruwaito cewa Joe ya caka wa Ibrahim Khalil Auwal wuka yayin faɗan. Daga nan aka garzaya da shi zuwa asibitin Abdullahi Makama da ke Dabai, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.

Bayan samun labarin mutuwarsa, wasu fusatattun matasa a yankin suka fusata inda suka kai wa Joe hari, suka kashe shi tare da ƙona gawarsa a kan babbar hanya.

“Gwamnatin ta bayyana wannan lamari a matsayin abin takaici matuƙa, wanda ba za a lamunta da shi ba, kuma ya saɓa da al’adun karamci da zaman lafiya da ake da su a Jihar Katsina”,Inji Dr Ɗanmusa.

Ya jaddada cewa lamarin laifi ne da ya samo asali daga rikicin kashin a tsakanin mutane biyu,don haka bai kamata a mayar da shi rikicin ƙabilanci ko addini ba.

“Gwamnatin Jihar Katsina za ta kamo duk masu hannu a cikin wannan tashin hankalin domin su fuskanci hukunci. Babu wanda yake da ikon ɗaukar doka a hannunsa. Za a gano tare da gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a harin farko da kuma kisan ramuwar gayya,”Inji kwamishinan.

Ya buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da gujewa yaɗa jita-jita ko bayanan ƙarya da ka iya tayar da hankali.

“An kuma tura jami’an tsaro zuwa yankin, inda ake gudanar da sintiri na haɗin gwiwa domin tabbatar da zaman lafiya da hana sake ɓarkewar rikici,”ya ce.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu tare da addu’ar Allah ya jiƙan su. Haka kuma gwamnan ya buƙaci shugabannin al’umma, na addini da sauran masu ruwa da tsaki da su bayar da haɗin kai wajen tabbatar da zaman lafiya da jituwa.

By ukarofi