
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyar adawa ta ADC kan dagewar da take yi na gudanar da taronta na kasa da babban taro duk da umarnin kotu da ya hana ta daukar irin wannan mataki.
INEC ta bayyana cewa 2cigaba da gudanar da tarukan duk da umarnin kotu na iya janyo mummunan hukunci na doka, har ma da yiwuwar haramta wa jam’iyyar shiga zaɓuka masu zuwa.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Juma’a, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya nesanta hukumar daga rikicin cikin gida da ke addabar ADC domin ana gudanar da shari’a a kotu akan shugabancin jam’iyyar.
Ya ce: “A ɓangaren mu, INEC na daga cikin bangarorin da ke cikin karar, domin wani dan ADC ne ya shigar da kara inda ya hada da INEC a matsayin wanda ake kara.
“Har ila yau, kotu ta bayyana ƙarara cewa bangarori, ciki har da David Mark, su guji ɗaukar duk wani mataki da zai ƙara rura wutar rikicin da ke gaban kotu.”
Ya yi gargadi cewa duk wani yunƙuri na cigaba da shirye-shiryen tarukan ya kamata a duba shi bisa la’akari da umarnin kotu da ke akwai.
Ya kara da cewa: “Idan har za su ci gaba da gudanar da taron su, ya rage nasu su duba ko hakan bai saɓa wa umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara ba.”
