Tinubu ya ƙaddamar da sabon babban ofishin Kwastom a Ogun

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabon ginin ofishin Hukumar Kwastom mai darajar Naira biliyan 73 a Jihar Ogun a wani mataki da ake ganin zai ƙarfafa ayyukan hukumar da kuma inganta ƙwarewar ma’aikatanta.

A yayin taron ƙaddamarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sabon ginin zai taimaka wajen ƙara inganci a harkokin kwastam musamman wajen sanya ido akan shigo da kaya da kuma hana safarar haramtattun kayayyaki.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa hukumomin gwamnati domin su yi aiki yadda ya dace da zamani.

Sabon ofishin zai samar da ingantattun kayan aiki na zamani da kuma muhalli mai kyau ga ma’aikata, wanda hakan zai taimaka wajen haɓaka ƙwarewa da ƙarfafa ayyukan su na yau da kullum.

A nasu jawabin, jami’an sun yaba wa wannan mataki, inda suka ce zai taimaka wajen inganta tsaro akan iyakoki da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga gwamnati.

Ana sa ran cewa wannan sabon gini zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma inganta tsarin kasuwanci a jihar da ma sassan Nijeriya.

By Babaji