Mu na aiki tuƙuru wajen kawo ƙarshen ta’addanci da garkuwa a Nijeriya – Tinubu

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa tana nan daram kan baƙarta na ganin bayan ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane da suka addabi sassan ƙasar nan, yana mai cewa ba za su taba nuna rago ko karaya ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ƙalubalen tsaro, inda ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ana nan ana ƙara azama wajen samar da dabarun yaƙi na zamani domin kakkabe ɓatagari.

Bayanai sun nuna cewa Shugaba Tinubu ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa shi ne babban nauyin da ya rataya a wuyansa, saboda haka ba zai amince da duk wani yunƙuri na tsoratar da al’umma da masu tayar da ƙura suke yi ba.

Rahoton ya nuna cewa shugaban ya jinjina wa jami’an tsaro bisa jarumtar da suke nuna wa a fagen fama, yana mai alƙawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da ba su dukkan goyon bayan da suke buƙata, kama daga kayan aiki zuwa jin daɗinsu.

Haka kuma, ya buƙaci ƴan ƙasa da su kasance masu bayar da haɗin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani motsi na ban-zara, domin a cewarsa, nasara a kan ta’addanci na buƙatar dukkanin al’umma su tashi tsaye.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na kallon waɗannan kalamai a matsayin wani saƙo mai ƙarfi ga ƙungiyoyin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane cewa lokacinsu ya kusa ƙarewa a ƙarƙashin wannan gwamnati.

A halin yanzu, ana sa ran ganin ƙarin sauye-sauye a ɓangaren tsaro da kuma yawaitar kai farmaki maɓoyar ƴan ta’adda a fadin jihohin da abin ya shafa domin tabbatar da kalaman shugaban ƙasar sun fito a aikace.

By Babaji