Kaduna: Harin ‘yan bindiga ya yi ajalin mutane bakwai da sace wasu a Kachia

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a ƙauyen Ariko da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna sun farmaki mutane a coci guda biyu yayin da ake bikin Easter a yau Lahadi, inda suak halaka mutane bakwai da yin garkuwa da wasu da dama.

Al’amarin ya faru ne a safiyar yau Lahadi, wanda ya jefa jama’ar yankin cikin firgici da jimami.

Kansilan yankin Awon da ke Gundumar Ariko, Mark Bawa ya tabbatar da harin ga manema labarai ta wayar tarho.

A cewarsa, cocin First Ekwa da St. Augustine Catholic ne aka kai wa harin waɗanda ke yankin Ariko, inda aka halaka mutane bakwai yayin da wasu suak yi ikirarin takwas ne.

Ya bayyana cewa, maharan sun zo a adadi mai yawa, inda suka zagaye yankin tare da yin harbe-harbe na kan mai uwa da wabi.

Mazaunin yankin sun ce, an ɗauki tsawon lokaci ana ruwa wuta ba tare da dakatarwa ba, wanda ke ƙara nuna yadda yankunan karkara a jihar ke zama cikin haɗari.

Wannan hari na zuwa ne ƙasa da wata biyu da aka yi irin sa a ƙauyen Kurmin Wali na ƙaramar hukumar, inda aka sace masu bauta da dama yayin da suke coci acikin watan Fabrairu, 2026.

By Babaji