
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Katsina ta kama mutane huɗu da hannu a aikin dabanci da ya yi ajalin mutuwar wani KC Joe a ƙauyen Kokami da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja.
A wata sanarwa da ya fitar, Kakakin rundunar, Abubakar Sadiq ya ce a yanzu haka mutane huɗu suan hannun hukumar kuma ana gudanar da bincike akansu.
Ya bayyana cewa, al’amarin ya faru ne bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin marigayin da wani mai suna Ibrahim Auwal wanda Joe ya halaka, lamarin da ya fusata matasa har suka yi sanadiyyar mutuwar Joe.
Faruwar haka ke da wuya jami’an tsaro suka garzaya yankin domin kwantar da hankulan jama’a.
Kwamishinan ‘yan sandan Katsina, Ali Fage ya yi alla-wadai da faruwar al’amarin, inda ya yi kira ga jama’a da su riƙa aiko wa hukumar dukkan rahotannin da suka shafi zamantakewarsu tare da ƙaurace wa ɗaukar doka a hannu.
A nata ɓangaren, Gwamnatin jihar, ta bakin Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Dakta Nasir Mu’azu Ɗan-Musa, ta yi tir da aukuwar iftila’in, wanda ya samo asali akan saɓani tsakanin mutane biyu, wato Ibrahim Auwal da Joe da aka sani da K.C. Jones akan sayen gari da ruwan leda a shagon K.C. Jones.
Ana cikin cacar baki a tsakaninsu ne sai Joe ya daɓa wa Ibrahim Khalil Auwal makami. Daga nan aka garzaya da shi asibitin Abdullahi Makama da Daɓai, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Akan haka ne wasu fusatattun matasa a garin suka haɗa kai, sannan suka je suka farmaki Joe tare da banka masa wuta a kan babban titin yankin.
