Atiku ya yi hayar kamfanin Amurka kan biliyan N1.65 don ɗaga darajarsa akan Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ba wani kamfanin ƙwararru na Amurka mai suna Von Batten-Montague-York kwangila, domin karewa da inganta martabarsa a Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa kwangilar da aka ƙulla tsakanin ɓangarorin biyu na da darajar dala miliyan 1.2, inda ake sa ran kamfanin zai taimaka wajen ƙarfafa sunan Atiku tare da tinkarar tasirinsa daga Gwamnatin Tarayya.

An ƙulla wannan yarjejeniyar ne a ranakun 9 da 10 ga Maris, 2026, tsakanin manajan kamfanin, Karl Von Batten, da kuma wani ɗan siyasar Nijeriya mai suna Fabiyi Oladimeji, kamar yadda TheCabel ta ruwaito.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027 a Nijeriya, inda manyan ‘yan siyasa ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinsu a ciki da wajen Nijeriya.

Ana sa ran kamfanin zai jagoranci haɗa Atiku zama da jami’an gwamnatin Amurka da ‘yan majalisar ƙasar domin tattaunawa akan yadda za a gyara da inganta hoton Atiku a idon hukumomi da jama’a a ƙasar.

By Babaji