Matar tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hajiya Hadiza Attahiru Jega, wadda matar tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa INEC, Farfesa Attahiru Jega ne ta rasu a yau Lahadi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya, lamarin da ya janyo alhini da jimami a tsakanin iyalai, abokai da al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Hajiya Hadiza Jega ta kasance mace mai kamun kai da kishin al’umma, wacce ta taka rawar gani wajen tallafa wa harkokin ilimi da zamantakewa musamman a lokacin da mijinta ke riƙe da mukaman gwamnati da na jami’a.

Farfesa Attahiru Jega, wanda ya taba zama VC a Jami’ar BUK da kuma shugaban INEC, ya samu jajen ta’aziyya daga manyan ‘yan siyasa, malamai da kuma al’umma daga sassa daban-daban na Nijeriya da ma wajenta.

Ana sa ran za a gudanar da jana’izar marigayiyar bisa koyarwar addinin Musulunci a Birnin Tarayya Abuja.

By Babaji