Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Farashin man fetur ya faɗi da kusan kashi 15 a ranar Laraba, bayan sanar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi tsakanin Amurka da Iran, wadda ake ganin za ta buɗe ƙofar tattaunawa domin rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.
Farashin Brent ya sauka ƙasa da dala $100 a kowace ganga a kasuwannin duniya da misalin ƙarfe 12:00 na dare (GMT), bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu da Iran, da sharadin cewa za a buɗe mashigar ruwa ta Hormuz gaba ɗaya.
Bayan da farashin ya kai har dala $111.80 a ranar Talata, ya rufe ciniki a kan $109.27. Amma da ƙarfe 6:34 na safe (GMT), farashin ya sauka zuwa $92.98, wanda ke nuna raguwar kusan kashi 15%.
A lokaci guda, farashin man West Teɗas Intermediate (WTI) ya kai dala $96.67 a kowace ganga.
Faduwar farashin ta biyo bayan sanarwar Trump na tsagaita wuta da Iran na makonni biyu, wanda ya danganta da cikakken buɗe mashigar Hormuz.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce tattaunawar da Pakistan ta shiga tsakani ta samar da sakamako mai kyau, sa’o’i kaɗan kafin wa’adin da ya bai wa Iran ya ƙare.
Ya ƙara da cewa Amurka ta karɓi shawarwari guda 10 daga Iran, waɗanda za su zama tushen tattaunawa, yana mai cewa ɓangarorin biyu sun kusa cimma yarjejeniya ta dindindin domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
A ɓangaren Iran kuwa, jami’anta sun bayyana cewa za su dakatar da hare-hare idan aka daina kai musu hari. Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce tare da haɗin gwiwar rundunar sojin ƙasar, za su tabbatar da zirga-zirga cikin aminci a mashigar Hormuz na tsawon makonni biyu.
