Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai bai wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, ya yi watsi da zargin da jam’iyyun adawa ke yi cewa jam’iyyar APC na ƙoƙarin zama ita kaɗai za a gani a takardar zaɓen 2027.
Dare ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada cewa babu wani shiri—na ɓoye ko na fili—da nufin takaita zaɓe ga jam’iyyar APC kaɗai.
“Babu wani tsari, ko a ɓoye ko a fili, na sanya APC ita kaɗai a takardar zaɓe. Akwai jam’iyyu 21 da aka yi wa rijista da za su fafata; kowacce jam’iyya na da damar tsayar da ɗan takara. APC ba za ta tsaya ta rufe ƙofa ba saboda wasu jam’iyyu na fuskantar matsaloli,” inji Dare.
Wannan martani na zuwa ne bayan zargin da kakakin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya yi a ranar da ta gabata, inda ya zargi APC da haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyun adawa domin kauce wa fuskantar gasa mai ƙarfi a zaɓen 2027.
Abdullahi, wanda shi ma ya bayyana a shirin Politics Today, ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu da APC na ƙoƙarin jefa Nijeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya kacal, yana mai alƙawarin cewa ADC za ta yi adawa da duk wani yunƙuri na hakan.
A cewarsa, shugaban ƙasar ya san cewa ba shi da farin jini, kuma binciken cikin gida na jam’iyyar APC ya jefa su cikin fargaba.
Sai dai Dare ya ƙaryata wannan zargi gaba ɗaya, yana mai cewa APC ba ita ke takaita sararin dimokuraɗiyya a ƙasar ba. Ya nuna cewa yadda ADC ke iya kai ƙorafi ga Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) cikin ‘yanci, hujja ce da ke nuna cewa dimokuraɗiyya na nan daram.
Ya ƙara da cewa ba APC ko Shugaba Tinubu ke jin tsoron ‘yan adawa ba, yana mai jaddada cewa yayin da shugaban ƙasa ke mayar da hankali kan mulki, jam’iyyar APC na tafiyar da harkokinta na siyasa yadda ya kamata.
Dare ya kuma musanta cewa APC na da hannu a rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa, inda ya bayyana halin da ADC ke ciki a matsayin abin da suka jawo wa kansu.
“Abin da kuke gani nan, su ne suka jawo wa kansu. Sun zaɓi shigowa ta bayan gida, sun yi watsi da cewa akwai ƙorafe-ƙorafe da ƙara a kotu.
“Sun ɗauka cewa saboda suna adawa za su yi ta magana da ƙarfi… abin da ya faru da ADC a watannin baya darasi ne na yadda ba a tafiyar da jam’iyyar adawa, yadda ba a kwace jam’iyya, da yadda ba a gudanar da jam’iyya,” inji shi.
Ya ƙara da cewa maimakon su zargi APC ko shugaban ƙasa, ya kamata ADC ta bi hanyar shari’a domin tabbatar da zarge-zargen da take yi.
