
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya sanar da soke duk wani alƙawarin bayar da biza, yana umartar masu neman aiki da su duba imel ɗinsu don ƙarin bayani akan ranakun da aka sake tsarawa.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Ofishin Jakadancin ya ce ayyukan biza za su cigaba a ofishin jakadancin Amurka da ke Legas.
Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba da izinin gaggawa ga ma’aikatan gwamnatin Amurka da danginsu su bar ofishin jakadancin da ke Abuja, yana mai ambaton taɓarɓarewar lamuran tsaro a sassan Nijeriya a matsayin dalilin ɗaukar matakin.
Ma’aikatar ta shawarci Amurkawa da su sake duba shirin tafiye-tafiye zuwa sassan ƙasar sakamakon laifuka, ta’addanci, sace-sace, da tashin hankali da ke addabar al’umma.
A wani ɓangare kuwa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake tabbatar wa ‘yan ƙasa da baƙi cewa har yanzu al’amuran ƙasar na cigaba da wakana yadda aka saba.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis ta mai taimaka masa harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim.
A cewar ministan, cibiyoyin al’umma a Nijeriya na cigaba da gudanar da harkokinsu ba tare da tsaiko ga gwamnati, harkokin tattalin arziƙi ko rayuwar yauda kullum ba.
Ya ƙara da cewa, hukumomin tsaro na aiki tuƙuru wajen ganin sun shawo kan matsalolin da ke addabar fannin ta hanyar amfani da dabarun zamani da haɗin-gwiwa a tsakanin su.
