Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya ce, yawan da Nijeriya ke samarwa ya ƙaru zuwa aƙalla ganga miliyan 1.7 a kullum. Wannan ya nuna ci gaban da aka samu daga shekarar 2022.
NNPC ya alakanta ci gaban da aka samu da inganta tsaron bututun man fetur da kuma ƙoƙarin yaƙi da masu satar mai da lalata bututun mai a yankin Neja Delta.
A yayin da yake magana a wani zaman tattaunawa game da samar da tsaro kan bututun man fetur ɗin Nijeriya da aka yi a majalisa a Abuja, shugaban kamfanin man fetur na ƙasa, Bashir Ojulari, ya bayyana cewa yawan man da Nijeriya ke samarwa ya ƙaru daga ganga 960,000 da take samarwa a kullum a 2022 zuwa mafi tsakatsakin ganga miliyan 1.71 da kuma ƙololuwar ganga miliyan 1.84 a shekarar 2025 a kullum.
Ya jadddada cewa wannan nasarar da aka samu na zuwa ne sakamakon aiwatar da dunƙulallen tsarin samar da tsaro a fannin makamashi da niyyar kare kayayyaki da gine-ginen ɓangaren makamashi.
A cewar Mista Ojulari, tsarin samar da tsaron ya haɗa da tsarin tafiyarwa da tattara bayanan sirri da tsaro da sa ido da da haɗa kai da masana’antu da da haɗin kan al’umma da ke zaune a yankunan don sa ido.
Tsarin a cewar Ojulari ya taimaka wajen magance satar man fetur da lalata bututun man fetur wanda ya daɗe yana mayar da Nijeriya baya wajen samar yawan man fetur ɗin da yakamata.
“An samu ci gaban nan ne saboda mataki da ƙoƙari da ake yi, ba kawai ya faru ba ne,” ya faɗa, yana mai cewa wannan mataki ne ya ƙarfafa wa masu zuba hannun jari guiwa a ɓangaren mai da iskar gas.
Tsawon shekaru, ɓangaren man fetur da iskar na Nijeriya ya sha fama da matsaloli masu yawa ciki har da matsalar satar mai da ta yi ƙamari da yawan fashe-fashen bututun man fetur da daɗaɗɗun kayayyaki da kashe kuɗaɗe masu yawa wajen samar da man.
Wannan dalili ya jawo raguwar man da Nijeriya ke samarwa. Masana sun alaƙanta matsalar da rashin kwanciyar hankali a yankin Neja Delta da rashin tsayayyiyar hanyar gudanarwa da rashin isasshen hannun jari da sauransu.
NNPCL ta sh nanata cewa satar man fetur a matsayin babban ƙalubale wajen samar da man fetur. A shekarar 2022 kaɗai, kamfanin ya ce ya yi asarar gangar mai 470,000 a kowacce rana da kuɗinsu ya kai Dala 700 a kowanne wata saboda haramtattun ayyuka.
Kamfanin man na ƙasashen waje ciki har da Shell sun sha fuskantar tsaiko saboda dambarwar lalata wa mazauna garuruwan muhallansu sakamakon kwararar mai. A akwai lokutan da aka dakatar da samar da mai a yankin Neja Delta saboda fashe-fashen bututun mai.
Haka kuma yawan kuɗin da ake kashewa wajen samar da tsaro na ƙara yawan kuɗin da ake kashewa wajen samar da man.
Haka kuma, hukumar kula da albarkatun man fetur ta ƙasa, ta rawaito cewa Nijeriya na tarin man a ajiye da ya kai ganga biliyan 37.01 kawo 1 ga watan Janairu 2026, wanda ya nuna raguwar da aka samu da kaso 0.74% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Wannan raguwa ta man fetur da aka samu na da alaƙa da irin ƙirdadon da aka yi wajen samar da man a shekarar 2025. Sai dai kuma yawan iskar gas ya ƙaru da daga kaso 2.21% zuwa kaso tiriliyan 215.19 na kubik-fit sakamakon gano wasu da inganta yadda ake adana iskar gas ɗin.
A yayin zaman tattaunawar dai, manyan jami’an gwamnati sun yi kira da a cigaba da irin ƙoƙarin da ake yi inda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wanda Jimoh Ibrahim, ya wakilta ya jaddada buƙatar samar da haɗin guiwa mai ƙarfi wajen kula da bunƙasar samar da mai.
Haka shi ma shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, wanda Julius Ihonɓbere, ya wakilta, ya buƙaci a tabbatar da adalci da shigo da kowa da kowa wajen aiwatar da tsare-tsare.
Kwamitin kula da man fetur na majalisar ne ya shirya taron wanda ya tattaro duk wasu ƙusoshi a fannin tsaro da masana’antar man fetur domin a yi nazarin ci gaban da aka samu da ƙarfafa amfani da dabaru da aka fitar.
Kamfanin NNPCL ya jaddada aniyarsa ta ƙarfafa haɗin guiwa da ɗorewar matakan tabbatar da tsaro domin ganin ɓangaren mai ya ci gaba da samun ci gaba.
