NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai ƙarfi na kwana uku a sassan Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Yanayi ta ƙasa (NiMet), ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa a sassa daban-daban na Nijeriya daga ranar Alhamis zuwa Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026.

A cikin rahoton yanayin da ta fitar a ranar Laraba, hukumar ta bayyana cewa ana sa ran samun iska a wasu jihohin arewacin ƙasar a ranar Alhamis, musamman a jihohin Borno, Yobe, Kano, Katsina, Zamfara, Jigawa, Kebbi da Sakkwato.

Sai dai daga bisani a wannan rana, ana iya samun tsawa mai ɗauke da ruwan sama a wasu yankunan jihohin Taraba, kudancin Bauchi, kudancin Kaduna, Adamawa da Gombe.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta yi hasashen yanayi mai haɗa yayyafi da hasken rana, tare da yiwuwar tsawa da safe a wasu sassan jihohin Neja, Kwara da Kogi. Haka kuma daga baya ana sa ran samun tsawa mai rauni da ɗan ruwan sama a jihohin Nasarawa, Fialto, Kwara, Kogi, Babban Birnin Tarayya Abuja da Benuwe.

A kudancin ƙasar, rahoton ya nuna cewa za a samu girgije tare da ɗan hasken rana, da yiwuwar tsawa da safe mai ɗauke da ruwan sama matsakaici a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Edo, Legas, Kuros Riba, Akwa Ibom, Bayelsa, Ribas da Delta. Daga bisani kuma ana sa ran tsawa da ruwan sama matsakaici a mafi yawan yankunan.

A ranar Juma’a, hukumar ta ce za a sake samun iska matsakaici a arewa, tare da yiwuwar tsawa da safe a wasu sassan Taraba da Adamawa. Daga baya kuma ana sa ran tsawa mai ɗauke da ruwan sama matsakaici a jihohin Taraba, Bauchi, Kaduna, Adamawa da Gombe.

A Arewa ta Tsakiya a ranar Juma’a, za a samu yanayi mai girgije da hasken rana lokaci-lokaci, tare da tsawa da safe a wasu yankunan Nasarawa da Benue, sannan daga baya tsawa da ruwan sama za su bazu a faɗin yankin.

A kudanci kuma, ana sa ran yanayi mai girgije da hasken rana tare da yiwuwar tsawa da safe a wasu sassan Edo, Ondo, Ogun, Legas, Kuros Riba, Akwa Ibom da Delta, sannan daga bisani a samu ruwan sama mai matsakaici a yankin baki ɗaya.

A ranar Asabar, NiMet ta yi hasashen samun iska kaɗan a arewa, yayin da yankin Arewa ta Tsakiya zai fuskanci hasken rana tare da ɗan yayyafi. A kudanci kuwa, za a samu yayyafi da hasken rana, tare da yiwuwar tsawa da safe a wasu yankunan Ondo, Ogun da Legas, sannan daga baya a samu tsawa da ruwan sama a yankin.

Hukumar ta shawarci jama’a da su kasance cikin shiri, musamman a yankunan da ake sa ran tsawa da ruwan sama, domin kauce wa haɗurra da kuma kiyaye lafiyarsu.

By ukarofi