
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), Dakta Patrice Motsepe, ya gana da jami’an ƙwallon ƙafa na ƙasar Moroko domin magance matsalolin rikicin Kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON).
Motsepe ya tabbatar da cewa CAf tana shirye-shiryen yin gyare-gyaren ga dokokin tsare-tsaren AFCON da kuma sanya hukunci mai tsauri domin kauce wa irin rashin ɗa’ar da ya faru a wasan ƙarshe na gasar a aka yi a Junairu.
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da kwamitin ɗaukaka ƙara na CAf ya yi na ƙwace kofin daga hannun Senegal da ts yi nasara a wasan da bai wa Moroko sakamakon fice a fili da ‘yan wasan Senegal suka yi ana tsaka da wasa.
Ziyarar ta zo ne a wani lokaci mai ɗauke da zafi, bayan CAF ta soke nasarar da Senegal ta samu da ci 1-0 a wasan ƙarshe da Morocco ta karɓi bakunci, wanda aka buga a ranar 18 ga Janairu.
CAF ta bayyana cewa ta dogara ne da dokokin wasan da suka shafi barin fili, inda daga bisani ta ba Morocco nasara da ci 3-0 a ranar 17 ga Maris.
Haka kuma, Motsepe ya ziyarci Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal a Birnin Dakar inda ya roƙi a haɗin kai tare da kira ga magoya baya da su mayar da hankali wajen ba ƙasashen Afirka goyon baya a wasannin gasar Kofin Duniya na 2026 da ke tafe.
