Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata kotun majistare da ke zama a Kano ta bayar da umarnin tsare wata matar aure mai suna Zayya Magaji bisa zargin kashe ɗan kishiyar ta.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wadda ake zargin, mazauniyar ƙauyen Danbango a ƙaramar hukumar Kabo, an gurfanar da ita a gaban kotu ne ta hannun mai gabatar da ƙara na jihar, Barista Muhammad Aliyu, inda aka karanta mata tuhume-tuhumen da ake yi mata.
Ana zargin cewa ta yi sanadiyyar mutuwar jaririn ɗan kishiyar ta mai kwanaki uku ta hanyar ba shi guba. Sai dai wadda ake zargin ta musanta zargin da ake yi mata.
Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotu cewa an tura kundin shari’ar zuwa Ma’aikatar Shari’a ta jihar domin samun shawarar doka.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Auwal Yusuf, ya amince da buƙatar dage shari’ar tare da bayar da umarnin tsare wadda ake zargin.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu domin ci gaba da shari’a.
