2027: APC ta nemi Shekarau ya dawo jam’iyyar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya kai ziyara jihar Kano domin jawo hankalin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, ya koma jam’iyyar.

Yilwatda, wanda ya jagoranci wata babbar tawaga ciki har da Sanata Hayatu Gwarzo, ya gana da Shekarau a gidansa da ke Mundubawa, inda ya bayyana cewa ziyarar na nuni da girmamawa da kuma kokarin hada kan manyan ‘yan siyasar Arewa gabanin zabuka masu zuwa.

Ya yaba da kwarewa da mutuncin Shekarau, yana mai cewa gudummawarsa na da matuƙar muhimmanci ga siyasar Nijeriya.

Haka kuma ya jaddada bukatar hadin kan Arewa domin tabbatar da ci gaba da kwanciyar hankali.

Shugaban na APC ya kuma ce ya kamata a bar mulki ya ci gaba a hannun Kudanci karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, yana mai nuni da yadda Arewa ta tsaya tsayin daka a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya lissafo wasu manyan ayyukan gwamnatin tarayya kamar layin dogo na Lagos–Kano–Maradi da kuma aikin bututun iskar gas, yana mai cewa za su bunkasa tattalin arzikin Arewa, musamman Kano.

A nasa ɓangaren, Shekarau ya gode da ziyarar, amma ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta PDP na fama da rikici mai tsanani, wanda ya kira “babbar cuta.” 

Ya ce yana tuntubar masu ruwa da tsaki kafin yanke shawarar makomarsa ta siyasa nan da kwanaki masu zuwa.

By ukarofi