Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
‘Yan bindiga ɗauke da makamai sun kashe mutane 21 a ƙauyen Bunkasau da ke ƙarƙashin gundumar Zarummai ta ƙaramar hukumar Bukkuyum, dake a jihar Zamfara.
Maharan waɗanda aka ƙiyasta sun haura 80, sun isa kan babura suka bude wuta kan mazauna yankin, sannan suka sace mutane da dama, galibi mata, sannan suka sace dabbobin su.
A cewar wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa, ya shaida wa Blueprint Manhaja ta wayar tarho cewa harin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na dare.
A cewarsa, mazauna yankin suna ci gaba da neman mutanen da suka ɓata a yayin harin.
Ya kuma nuna cewa ana ci gaba da shirye-shiryen jana’izar mamatan.
Hakazalika ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na Zamfara da su taimaka musu ta hanyar tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.
“Ina kira ga hukumomi musamman gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su tura ƙarin jami’an tsaro zuwa ƙaramar hukumarmu don magance matsalar rashin tsaron da ke addabarmu”. Ya ce
Lokacin da Wakilin mu ya tuntuɓe shi, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda Jihar DSP Yazid Abubakar ta hannun wakilinmu ya tabbatar da lamarin..
A cewar sa, waɗanda suka rasa rayukan su ba a tantance adadin su ba, kuma rundunar tuni ta tura Jami’ai isassu don kare rayukan al’ummar yankin.
DSP Yazid Abubakar ya ƙara da cewa, komai ya dawo daidai a yankin, yana mai kira ga alummar jihar dasu riƙa bawa rundunar yan sandan jihar goyon bayan da ya dace wajen bada bayanan sirri na maɓoyar yan ta’addar don ɗaukar matakin da ya dace.
Ƙaramar hukumar ta Bukkuyum dai a baya bayan nan tana shan fama da matsalar hare haren yan ta’adda, yayin dan ko a satin da ya gabata yan ta’addar sun yi garkuwa da mutane sama da 150.
