Jami’ar Sule Lamiɗo ta yaye ɗalibai 4,109 a karo na biyu tun bayan kafa ta

Spread the love

Daga ABUBAKAR M TAHEER

Ilimi shine babban abinda Gwamnatin Jigawa take saka hannu jari mafi tsoka inji Gwamna Umar Namadi.

Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa ta gudanar da taron yaye ɗalibai a karo na biyu tun bayan buɗe jami’arba shekarar 2013.

Taro da ya haɗe ɗaliban da suka kammala jami’ar tun daga 2018 zuwa 2025 wanda ya ƙunshi ɗalibai 4,109 a shekaru 6 ya samu halartar manyan yan siyasa, jami’an gwamnatin, Farfesoshi da sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban a faɗin ƙasar nan.

Da yake gabatar da jawabinsa Gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar Namadi Ɗan Modi ya bayyana cewa gwamnatin sa tana zuba makudan kuɗaɗe a ɓangaren ilimi domin shine hanya mai ɓullewa wajen samar da cigaba mai ɗorewa ga jihar ta Jigawa.

Gwamna ya bayyana cewa wannan taro ba wai yaye ɗalibai bane wata haɗuwa ce wanda zamu tuna irin nasarar da jami’ar jiharmu ta samu bayan samar da ita sama da shekaru 10 wajen samar da haziƙan ɗalibai da masana a ɓangarori daban-daban.

Gwamna ya ƙara da godewa wanda suka tsaya tsayin daka wajen samar da jami’a wanda yanzu haka ake ganin abinda suka shuka na alkairi.

Gwamna ya ƙarƙare da jan hankali ɗaliban da su mayar da hankali wajen amfani da ilimi da suka samu wajen nazari, bincike da samar wa kansu hanyoyin dogaro da kai domin ciyar da jami’ar gaba.

Haka kuma an gudanar da karrama Sarkin Katagum Alhaji Umar Faruq na biyu OON, a matsayin shugaban jami’ar ta Lamiɗo inda aka karramshi da digirin girmamawa.

An kuma karrama daraktan cibiyar bada agaji ta Qatar Charity Foundation a Nijeriya Mr. Hamdi El-Sayyid Abdou da digirin girmamawa sai kuma Mr. Hisham Muhammad Abdussalam Director World Assembly of Muslim Youth (WAMY) shima da digirin girmamawa.

By ukarofi