Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Dr. Abdulmudallib Muhammad Gusau, fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Zamfara, ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Zamfara a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ta ADC.
Ya yi wannan sanarwar jim kaɗan bayan yin rijista a matsayin mamba a jam’iyyar ta ADC a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau yau Litinin.
A cewarsa, rashin shugabanci mai kyau, rashin aikin yi da rashin jajircewar shugabanni a Jihar su ne manyan abubuwan da suka haifar da ƙaruwar rashin tsaro a jihar.
Ya yi alƙawarin canza alƙiblar jihar Zamfara ta hanyar magance matsalar rashin tsaro da kuma haɓaka ci gaban tattalin arziki da zamantakewa idan ya zama gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC a zaɓe mai zuwa.
Dr. Gusau wanda ya soki gwamnatin jihar kan yin sakaci kan batutuwan tsaro kuma ta gaza magance matsalar ‘yan bindiga dake kawo asarar rayukan alummar Jihar, ya bayyana cewa zai kawo ƙarshen rashin tsaro cikin ɗan gajeren lokaci.
Dangane da makomar jam’iyyar ta ADC, Dr. Gusau ya dage cewa yana da yaƙinin cewa ADC za ta iya kawo sauyi mai kyau ga Jihar Zamfara a shekarar 2027.
A cewarsa, ADC ita ce jam’iyyar siyasa ɗaya tilo da ke da kyakkyawan fata don cigaban ƙasar nan a zaɓen dake tafe.
Yayi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su gaggauta yin rijista don samun nasarar jam’iyyar a Jihar.
