Gwamnatin Katsina ta amince da tallafa wa gidauniyar tsaro da Naira biliyan ɗaya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da buƙatar gwamnatin jihar na bayar da gudummawar naira biliyan ɗaya domin tallafawa gidauniyar tsaro ta jihohin Arewa, da nufin inganta tsaro a yankin.

Wannan mataki ya biyo bayan wata buƙata da Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gabatar wa majalisar, inda ya nemi amincewarta bisa tanadin doka.

A zaman majalisar wanda Kakakin Majalisa Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya jagoranta, an tattauna batun tare da amincewa da shi baki ɗaya.

Takardar wadda shugaban masu rinjaye, Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai ya gabatar, ta nuna cewa gwamnatin jihar za ta bayar da naira miliyan 300, yayin da kananan hukumomi 34 za su samar da sauran naira miliyan 700 domin cika jimillar naira biliyan ɗaya.

Bayan amincewa da wannan buƙata, Kakakin Majalisa ya umarci a tura ƙudurin zuwa ɓangaren zartaswa domin fara aiwatar da shi.

A gefe guda, majalisar ta buƙaci ɓangaren zartaswa da ya ɗauki matakin gaggawa wajen gyara matsalar zaizayar ƙasa da ke addabar hanyar Eka zuwa Kadandani, Kuraye da Yargamji, a ƙananan hukumomin Batagarawa, Rimi da Charanchi.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Charanchi, Hon. Lawal Isah Kuraye, ya bayyana cewa an kammala aikin hanyar tun shekarar 2017 a zamanin gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari, amma yanzu tana fuskantar matsalar zaizayar ƙasa a wasu sassa, wanda ke buƙatar gyara cikin gaggawa.

Haka kuma, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kaita, Hon. Surajo Abdu Kwaskwaro, ya gabatar da ƙuduri na buƙatar gyaran Makarantar Firamare ta Dono da ke mazaɓar Dankaba.

Ya bayyana cewa ɗalibai daga aji na daya zuwa na shida suna karatu ne a cikin aji guda ɗaya sakamakon ƙarancin ɗakunan karatu, sannan makarantar na bukatar rijiyar ruwa domin rage wahalar samun ruwa da daliban ke fuskanta.

A ƙarshe, majalisar ta amince da waɗannan ƙudurorin tare da umartar a miƙa su ga ɓangaren zartaswa domin ɗaukar matakin da ya dace.

By ukarofi