Gwamnan Katsina ya jagoranci zama na musamman kan matsalar faɗan ƙauraye

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya gudanar da wani muhimmin taro da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin tattauna hanyoyin magance matsalar faɗan kauraye da ake fama da ita a cikin garin Katsina.

Taron ya haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad, ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Hon. Ali Abu Albaba, Kwamishinan ƴan sanda, sauran shugabannin hukumomin tsaro, da masu unguwanni.

Yan kwanakin nan faɗan ƙauraye yayi ƙamari musamman a wuraren Farin Masallaci,Yan wanki, Yan Taba da wasu sassa duk a unguwar unwala.

Faɗace faɗacen da ake danganta da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ya haddasa mutuwar mutane da dama da jikkata wasu a unguwar.

Duk da jami’an tsaro na iyaka bakin ƙoƙarin su wasu mutane mazauna unguwar na ganin idan ba an magance matsalar masu sha da dillancin ƙwayoyi a unguwar ba ta ba a rabu da bukar ba.

Wata matsalar da ake zargin ƙaurayen shine na ƙwacen wayar hannu da sarar mutanen da basu ji ba basu gani ba.

By ukarofi