Askarawan Zamfara sun kama mutane takwas da ake zargi da haɗa kai da ‘yan ta’adda a Gusau

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jami’an tsaron al’umma na Jihar Zamfara watau Community Protection Guard (CPG) sun kama mutane takwas da ake zargi da taimakawa ‘yan ta’adda a Gusau.

Kwamandan na CPG, AIG Muhammad Shehu Dalijan mai ritaya, ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a gaban ‘yan jarida a hedikwatar CPG da ke Gusau a yau, Laraba.

A cewarsa, CPG ta yi nasarar kama wata mota ɗauke da sabbin babura guda uku, wani na’urar fashewa (IED), da kuma tsabar kudi da suka kai Naira miliyan 13,500,000 da ake zargin za a kai wa ‘yan ta’adda a ƙauyen Bindin, a ƙaramar hukumar Maru.

Ya ƙara da cewa an kama nakiya 98 ta dynamite, masu fashewa 25, da kuma na’urori 25 daga hannun waɗanda ake zargin.

A cewarsa, ana kyautata zaton ana kyautata zaton kayayayykin za su kaiwa ‘yan ta’adda ne don musanya su da zinare.

“Muna zargin yan ta’adda za su yi amfani da ababen fashewar a kan tituna don kashe jami’an tsaro,” in ji Dalijan.

Ya ce bayan kammala bincike na farko, za a miƙa waɗanda ake zargin ga hukumar ‘yan sanda domin a ɗauki matakin shari’a yadda ya kamata.

Kwamandan ya yi alƙawarin cewa CPG za ta yi aiki dare da rana don tabbatar da cewa “‘yan ta’adda ba su da wani wurin ɓuya a jihar.”

Ya sake nanata cewa rundunar za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya a Jihar Zamfara.

Ya kuma roƙi mazauna jihar da su goyi bayan rundunar ta hanyar samar da bayanai masu amfani game da ƙungiyoyin ta’addanci don mayar da don daukar cikin gaggawa.

A wata hira da aka yi da shi, wanda ake zargi direban motar da aka kama, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Abubakar Abdullahi Dangulbi, ya bayyana cewa ya karɓi kayan da sauran wadanda ake zargin don kai su ga mai shi a ƙauyen Bindin.

By ukarofi