Danmadamin Birnin Magaji: Ba don ku ba da ruwa ya ci tarihin adabin baka 

Spread the love

Daga NASIR WADA KHALIL PhD

Wato Mai Girma Alhaji Ibrahim Muhammad ɗanmadamin Birnin Magaji ya wuce a ce masa Malamin Adabi sai dai ko Jami’ar Adabi. Duk inda aka gudanar da bincike akan kiɗa, waƙa ko tarihi daga Arewacin Najeriya zuwa Kudancin Niger sai an samo shi taron zai cika. 

Baya mantuwa na shekarar faruwar abu ko sunan muhalli ko jerin yadda abu ya faru sannan kuma baya kiwar rubutu, komai yana ba shi haƙƙinsa. 

Ya taimaka wajen buɗe sabon shafi na yadda ake kiran makada ta hanyar jingina  nasabarsu da garinsu misali Salihu Jankidi Rawayya, Musa Dankwairo Maradun, Muhammadu Bawa Dan’anace Yartsakkuwa Gandi da sauransu. Yanzu ana fadar makadi kasan daga inda ya futo saɓanin da sunansa ne kurun za a bayyana. 

Ga inda jami’oinmu za su bada digirin digirgir a bisa hujja, domin abinda ɗanmadamin Birnin Magaji ya ke yi ya dace da matsayar Majalisar ɗinkin Duniya ta UNESCO a taronta na duniya na shekarar 2003 (2003 UNESCO CONɓENTION) domin taskace da wanzar da al’adun da hannu baya taɓa wa kamar kiɗa, waƙa, biki da sauransu (Safeguarding Intangible Cultural Heritage of  Humanity).

Tare da haɗin hannu da jami’o’i musamman Jamiar Usumanu ɗanfodiyo ɗanmadami ya taimaka wajen wanzar da tarihi da fasaha da gudunmowar waɗannan makaɗa ko mawaƙa na ƙasar Hausa waɗanda suka yi rayuwa tsahon zamani da ya zarta a ƙarni ɗaya (Shekara 100).

Wannan gudunmowa zata ci gaba da amfanar yara masu tasowa wajen sanin hikima da fasahar harshe da tarihi da sanin harshe da kalmomin da kuma sanin cewa muma Allah ya horr mana fasihai kamar yadda ake samu a sauran ƙasashen duniya.

Ina daɗa yaba wa Mai Girma ɗanmadamin Birnin Magaji a bisa wannan muhimmiyar gudunmowa da yake bayarwa da kafafen radiyo da talabijin da kafofin sadarwa na zamani da kundayen bincike da jami’o’i da manazarta suke samarwa.

Ma’assalam.

By ukarofi