Daga MUKHTAR YAKUBU
Hauwa Shehu tana ɗaya daga cikin marubuta ƙirƙirarren labarin da a yanzu suke sahun gaba musamman dai a soshiyal midiya.
Ta yi rubutu masu yawa da waɗanda aka buga a littafi da kuma na soshiyal midiya. Wannan ya ba ta damar shiga gasanni da dama na ƙirƙirarren labari. Ita ce ta zo ta uku a gasar marubuta ta Hukumar tace finafinai da aka gudanar a shekara ta 2024 da sauran gasar da ake yi ta marubuta.
Domin jin ta bakinta, mun tattauna da ita domin jin yadda ta fara rubutun da irin damar da ta samu a cikin harkar, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.
HAUWA SHEHU: Sunana Hauwa Shehu ni ‘yar asalin Jihar Kano ce, na yi makarantar firamare da ƙaramar sakandire (Jss) a nan Jihar Kano, babbar sakandire (SSS) kuma a Jihar Kaduna.
Na samu zarafin kammala degree na farko a fannin koyar da ilimin lissafi ‘Bsc.ed Mathematics’.
Ko ya aka yi kika samu kanki a cikin harkar rubutu?
Na samu kaina da sha’awar harkar rubutu tun daga makaranta firamare a lokacin da na fahimci zan iya kai koke na ta hanyar jera kalmomi a takarda ba tare da na furta su da baki ba. Daga nan na fahimci rubutu babbar hanya ce ta isar da saƙo, ilimantarwa, faɗakarwa tare da nuni cikin nishaɗi. Daga lokacin na fara gwada alƙalamina.
Ko a wacce shekarar kika fara rubuta littafi?
A shekarar dubu biyu da tara 2009 bayan kammala sakandire a lokacin ina zaman jiran sakamako. ‘Shukuriyya’ shi ne cikakken labarin da na fara rubutawa.
Ko kin taɓa buga littafi?
Eh, na taɓa buga littafin ‘Harin Gajimare’ sai kuma ‘Tsanin Tsaro’.
A shekarar da ta gabata kin shiga gasar marubuta ta Hukumar tace finafinai wadda kika zo ta uku. Ko ita ce farkon gasar da kika fara shiga?
Haka ne. A’a wannan ba shi ne karo na farko da na fara shiga gasa ba. Domin a shekarar 2023 na shiga gasar Gusau Institute kuma cikin ikon Allah ni ce na zo ta ɗaya. Na shiga gasar Marubuta GROUP shi ma na zo ta huɗu da labarin ‘Tukunyar Talaka’, na kuma shiga gasar Hikayata labarina na ‘Duniyar Sama’ ya fito a cikin jerin waɗanda suka cancanci yabo.
Wanne buri kike da shi a kan harkar rubutu?
Burina shi ne saƙonni da suke ƙunshe a rubutana su kasance masu tasiri ga al’umma. Ina son na zama marubuciyar da ko bayan raina za a rinka tunawa da saonnin da ta isar.
Waɗanne matsaloli ne marubuta suke fuskanta a wannan lokacin?
A ganina matsalolin da marubuta suke fuskanta a wannan zamani bai wuce ƙarancin tallafi da kuma ƙaracin fahimtar hanyoyin da za su bunƙasa basirarsu da yadda za su ɗaga darajar baiwarsu har su ci gajiyarta ba.
Wanne kira za ki yi ga marubuta?
Kiran da zan yi ga marubuta shi ne su rungumi sauyin da zamani ya zo da shi, ba tare da sun manta da ainihin darajar da alƙalaminsu ke ƙunshe da shi ba. Sannan su ci gaba da inganta basirarsu ta hanyar karatu, bincike da nazari. Ƙari a kan hakan su tsaftace rubutunsu.
To madalla mun gode.
Ni ma na gode.
