Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya halarci jana’izar Hajiya Hauwa (Maijidda) Abdulkadir Mamman Nasir, matar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Katsina, Alh. Abdulkadir Mamman Nasir wadda Allah ya yiwa rasuwa.
An gabatar da sallar jana’izar a masallacin GRA dake cikin birnin Katsina inda daga bisani aka birneta a maƙabartar Gidan Dawa duk a cikin garin Katsina.
Dubban mutane daga wurare daban-daban ne suka halarta daga abokan aiki, yan siyasa, jami’an gwamnati, yan uwa da abokan arziki da sauransu.
Anyi addu’o’in neman gafara ga marigayiyar tare da fatan Allah ya sa aljanna ce makomarta da magabata gaba daya.
