Zulum da jagororin tsaro sun halarci jana’izar janar da wasu sojoji da suka rasu a yaƙi da Boko Haram a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba aka yi jana’izar Birgediya Janar Omo Braimo, Kyaftin Ismail da wasu dakarun tsaro da suka rasu a yayin yaƙi da ta’addanci a Nijeriya.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da jami’an sojoji daga matakin jiha da kuma ƙasa.

An yi jana’izar ne a maƙabartar sojoji ta Maimalari da ke Maiduguri, inda aka samu halartar masu jimami daga sassan Nijeriya daban-daban domin jinjina wa sadaukarwar da dakarun suka yi a bakin aiki.

Daga cikin waɗanda suka je taron akwai Gwamna Umara Babagana Zulum na Jihar Borno; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Sanata Ali Ndume da dai sauransu.

An ga yadda aka karrama sadaukarwar mamatan yayin da Nijeriya ke cigaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya suka haddasa da ke addabar al’umma a sassan ƙasar.

By Babaji