CAC ta tabbatar da kutse a matattarar bayananta, ta shawarci jama’a su kula

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da harkokin kasuwanci da masana’antu (CAC) ta bayyana cewa tana gyara akan wani al’amarin tsaron sashen yanar gizonta da ya fuskanci kutse a wani sashe na matattarar bayananta.

A wata sanarwa da aike wa manema labarai a ranar Laraba, hukumar ta ce kutsen ya shafi wani ƙaramin sashi ne na matattarar, inda ta ce tuni ta ɗauki matakin gaggawa yayin da ta gano al’amarin.

CAC ta kuma ce tana aiki da Hukumar Ci-gaban Fasahar Sadarwa (NITDA) tare da wasu hukumomin gwamnati da wasu ɓangarori domin gano mataki da tasirin al’amarin.

A cewarta, ta ɗauki matakan da suka dace wajen ganin da guje wa sake shiga irin tarkon.

Yayin da ake cigaba da bincike, hukumar ta shawarci masu amfani da shafinta na yanar gizo da su ɗauki matakan kula domin bai wa bayanansu kariya.

Haka kuma, ta kirayi masu ruwa da tsaki da su kula da kundin bayananta, sabunta mashigar bayanai da kuma cigaba da kasancewa cikin sanya ido akan hada-hadar sadarwa da ba su hallata ba.

Kazalika, hukumar ta jaddada aniyarta ta cigaba da bai wa kundin bayanan jama’a kariya.

By Babaji