NAHCON ta gargaɗi maniyyata akan wakilan bizar ƙarya, ta ce Saudiyya ta rufe bayarwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta aike da saƙon gargaɗi game da damfara da wakilan tafiye-tafiye da shafukan sada zumunta na bogi ke yi, waɗanda ake zargin su da iƙirarin samar da bizar zuwa aikin hajji duk da cewa ƙasar Saudiyya ta rufe bayarwa a hukumance.

A cewar NAHCON, hukumomin Saudiyya sun rufe aikin bayar da biza tun a ranar 1 ga watan Shawwal, 1447, wato 20 ga Maris, 2026, lamarin da ke nuna kawo ƙarshen aikin neman biza ga maniyyatan bana.

Hukumar ta kuma sanar da cewa, tun gabanin wa’adin rufewar ya cika, an shigar da bayanan maniyyatan da aka tantance a na’ura tare da aika su ga hukumomin ƙasar.

Haka kuma, ta ce babu wani tsarin biza da za a amince da shi wajen yin hajjin na bana bayan wanda aka samar daga hukumomin.

Kazalika, ta ce akwai hukuncin mai tsauri da hukumomin Saudiyyan suka samar akan dukkan waɗanda aka kama suna aikin hajji ba tare da cika sharuɗɗa ko ƙa’idojin da aka gindaya ba, ciki har da zaman gidan yari na wata shida, tarar Riyal 20,000 (daidai da Naira miliyan 8.15), kora da kuma dakatarwar sake shiga ƙasar na tsawon shekara 10.

Tuni dai hukumomin suka shawarci al’umma da su kiyaye wajen tuntuɓar sahihan fagage da hukumomin jigilar alhazai, inda suka yi gargaɗi akan biyan kuɗaɗe ga wakilan bogi da ke ƙaryar samar da biza.

Don haka ne NAHCON ta nemi jama’a da su kasance masu lura tare da aiko da rahoton dukkan masu ayyukan bogi akan al’amarin ga hukumomin da suka dace.

By Babaji