
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta miƙa wanda ake zargi da hannu a manyan laifuka mai suna Mathew Chukwuemeka Adebiyi ga ƙasar Birtaniya domin ya fuskanci gurfanarwa akan zarge-zargen kisa da safarar miyagun ƙwayoyi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anthony Okon Placid ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis ta sahihin shafin hukumar na dandalin Facebook.
A cewar sanarwar, an gudanar da haka ne ta Cibiyar ayyukan hukumar ta kula da lamuran ƙasa-da-ƙasa (NCB) a Abuja, bayan buƙatar da hukumomin Ingila suka miƙa a watan Satumbar 2024.
Hukumomin ‘yan sanda sun zargi Adebiyi da hannu a kisan wani Joshua Boadu a ranar 18 ga watan Yunin 2018 a Birtaniya.
Haka kuma ana zargin sa da aikata laifin raba wani nau’in hodar iblis na musamman a tsakanin shekarar 2017 da 2018.
Bayan haka, wanda ake zargin ya tsere zuwa Nijeriya domin guje wa kamu, amma daga bisani a ranar 23 ga watan Junairu, 2025, jami’an INTERPOL na NCB Abuja sun yi ram da shi.
Akan haka ne wata Babbar Kotun Tarayya a Legas ta yanke hukuncin damƙa shi ga hukumomin Birtaniyar domin gudanar da shari’a akansa.
