Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An yaba wa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa da ya kafa dokar ta ɓaci akan ƙauraye da bangar siyasa a jihar.
Shugaban cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman ya faɗi haka a hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce wannan doka babu shakka za ta taimaka wajen dawo da zaman lafiya a wasu sassan jihar musamman cikin garin Katsina inda faɗace faɗacen ƙauraye ya yi ƙamari.
Kwamred Suleiman ya bayyana dillanci da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi kusan sune musabbabin ƙaruwar faɗace faɗacen ƙauraye a jihar.
Sai yayi kira da jami’an tsaro da su tashi tsaye wajan gano dillalan ƙwayoyin waɗanda a cewar sa mafi yawan su matasa ne kuma an san su a unguwanni su.
“Mafi yawan waɗannan matasa da ke wannan mummunar sana’a a gidajen suke sai dawa a gaban iyayensu,ba tare da an tsawa ta masu ba,”Inji Suleiman.
Haka kuma kwamred Suleiman yayi kira ga shugabannin tsaro musamman hukumar NDLEA da na yan sanda da su bincika yadda ake amfani da wasu jami’an su wajen taimakawa musu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Ya jinjina wa Gwamna Dikko Raɗɗa da sauran jami’an tsaro a jihar da suka tashi tsaye a yan kwanakin nan domin magance ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Shugaban ƙungiyar ya ƙalubalanci masu unguwanni da su taimakawa jami’an tsaro wajen bada bayanan sirri da za su taimaka wajen gano waɗannan ɓata gari.
Ya jaddada ƙudirin ƙungiyar sa na haɗa gwiwa da gwamnatin Katsina da jami’an tsaro wajan tabbatar da dauwamamman zama lafiya a jihar.
