Tallafin lantarki ya kai biliyan N418 yayin da fannin ya yi asarar biliyan N300 – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani rahoto ya nuna cewa ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya na ci gaba da fuskantar manyan ƙalubale na kuɗi da aiki, inda Gwamnatin Tarayya ta kashe kusan Naira biliyan 418.79 a matsayin tallafi a ƙarshen shekarar 2025.

Wannan bayani ya fito ne daga rahoton ƙarshen shekarar 2025 da Nigerian Electricity Regulatory Commission ta fitar, wanda ya yi cikakken bayani kan raguwar kuɗaɗen da ake tarawa, asarar da ake samu a rarraba wuta, matsalolin rashin daidaiton tashoshin lantarki, da kuma ɗan raguwar ƙarfin samar da wuta.

Rahoton ya bayyana cewa kamfanonin samar da wutar lantarki sun fitar da takardun kuɗin da suka kai Naira biliyan 804.93 kan wutar da suka samar a wannan lokaci. Sai dai saboda rashin daidaiton kuɗin wuta da ba ya nuna ainihin kuɗin samarwa, gwamnati ta dauki nauyin sama da rabin kuɗin, wato kashi 52.30 cikin 100.

Hukumar ta ce rashin tsarin kuɗin wuta da ya dace da gaskiyar farashi a dukkan kamfanonin rarraba wuta (DisCos) ne ya tilasta gwamnati ɗaukar wannan nauyi. Duk da cewa an samu ɗan sauki idan aka kwatanta da zangon baya, inda tallafin ya ragu da kusan Naira biliyan 39.96, har yanzu nauyin yana da girma.

Duk da wannan tallafi, ɓangaren ya ci gaba da fama da matsalolin rashin inganci a harkokin kasuwanci. Rahoton ya nuna cewa duk da wutar da aka kai wa kamfanonin rarraba wuta ta kai Naira biliyan 969.19, kuɗin da aka caje masu amfani bai wuce Naira biliyan 795.06 ba. 

Wannan ya nuna cewa akwai giɓin kashi 17.97 cikin 100 a lissafin kuɗin wutar da aka rarraba.

Sakamakon haka, kamfanonin rarraba wuta sun yi asarar Naira biliyan 174.12 a fannin lissafin kuɗin wuta kaɗai. Haka kuma, an samu ƙarin asarar Naira biliyan 139.19 sakamakon haɗaɗɗen asarar fasaha, kasuwanci da kuma rashin karbar kuɗi yadda ya kamata (ATC&C), wanda ya kai matsakaicin kashi 34.9 cikin 100.

Idan aka haɗa waɗannan asarori, jimillar asarar da aka samu ta haura Naira biliyan 300 a cikin wannan zangon.

A ɓangaren aiki kuwa, rahoton ya nuna cewa duk da ƙaruwar samar da wuta zuwa gigawatt-hour 9,831.58, akwai ci gaba da matsaloli a daidaiton tsarin grid. Sau da dama, mitocin lantarki sun faɗi ƙasa da ko kuma sun haura iyakar da aka amince da ita, abin da ke nuna rashin kwanciyar hankali a tsarin.

Haka kuma, an samu wani tangarda a tsarin wutar lantarki a ranar 29 ga Disamba, wanda ya haifar da wani ɓangare na faɗuwar grid.

Rahoton ya kuma nuna cewa kamfanonin rarraba wuta sun kasa cika nauyin da ake buƙata na biyan kuɗaɗe ga masu samar da wuta, inda suka biya Naira biliyan 437.27 kacal daga cikin Naira biliyan 471.66 da ake bukata, abin da ya bar giɓin Naira biliyan 34.39.

A ƙarshe, hukumar ta yi gargaɗin cewa tsarin tallafin da gwamnati ke dauka a yanzu yana barin baitul malin ƙasa cikin haɗari, saboda ba a kayyade shi ba, kuma yana iya ƙaruwa ko raguwa ba tare da tsari mai ɗorewa ba.

Duk da cewa an samu dan sauƙi sakamakon ƙarin wutar da aka ware wa masu amfani na Band A, rahoton ya jaddada cewa ɓangaren wutar lantarki na Nijeriya har yanzu na buƙatar manyan gyare-gyare domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabarsa.

By ukarofi