‘Yan bindiga sun sace mahaifin marubuciya Hadiza Auta

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da Dagacin Sabon Garin Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara,Alhaji Ibrahim Dan-Auta, wanda mahaifi ne ga wata fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, Hadiza Ibrahim D. Auta.

Tun da sanyi safiyar jiya Lahadi 19 ga Afrilu, 2026 ne marubuciyar ta fitar da wani rubutu a shafukanta na zaurukan sada zumunta, inda take bayyana labarin sace mahaifin nata da ƴan bindiga su ka yi. Ta rubuta cewa, ‘Inna Lillahi wa inna ilaihirraji’un! Ɓarayi sun tafi da babanmu.’

Wannan sanarwa ta ɗaga hankalin marubutan Hausa da dama, waɗanda suka yi ta aika saƙon jaje da addu’o’in samun kuɓutarsa daga hannun waɗannan miyagu.

Rahotanni sun bayyana cewa, ƴan bindigar da yawan su ya kai kimanin 10 sun shiga gidansa ne da ke unguwar GRA Lowcost wanda ke kusa da wani sansanin sojoji, da misalin ƙarfe 2 da rabi na dare, suna ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, kuma sun tafi da shi ne tare da matarsa a farko, yayin da yaransa suka fice ta katanga don tserar da rayuwarsu. Sai dai daga baya matar ta koma gida bayan da ƴan bindigar suka sake ta.

Sai dai iyalin wannan dattijo mai shekaru 80, wanda ke riƙe da sarautar Sarkin Yamma, sun nuna rashin jin daɗin su yadda aka kasa kai musu ɗauki akan lokaci bayan da ɗaya daga cikin iyalin gidan ya yi gaggawar zuwa kai rahoto wajen sojojin dake kusa da su, a lokacin da ƴan bindigar ke cikin gidan. Amma har suka ta fi babu wanda ya je, kuma ko da suka ta fi ba a iya gano inda suka bi ba, duk kuwa da kasancewar an ce da ƙafa suka tafi da shi, ba su shiga da abin hawa ba.

A cikin takaici da alhini, Hadiza D. Auta ta ce, ‘Abin da muke jin sa a nesa yau ga shi har cikin gidanmu!’

Har kawo lokacin haɗa wannan rahoto ba a ji wani bayani daga wajen ƴan bindigar ba, sai dai jama’a na cigaba da addu’o’i, da jajentawa marubuciyar da sauran iyalinsa.

By ukarofi