Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan takarar kujerar majalisar Dattijai a Katsina ta tsakiya injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya kammala rangadin ƙananan hukumomi 11 da ke Katsina ta tsakiya.
Injiniya Darma wanda ya fito takarar kujerar Sanata a jihar Katsina ƙarƙashin jamiyar APC ya kai ziyarar a ƙananan hukumomin ne domin neman goyon bayan shugaban jam’iyar a gabanin zaɓen fidda gwani.
Ya nuna godiya matuƙa kan yadda ya samu kyakkyawar tarba a ƙananan hukumomin 11 na shiyyar Katsina da ya ziyarta domin tuntuba, a cewar sa
Ɗan takarar, kuma tsohon shugaban asusun bunƙasa kimiyyar man fasahar man fetur ta ƙasa, Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana jin daɗin sa bisa yadda shugabannin da magoya bayan jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi suka nuna masa ƙauna da soyayya wanda a cewar sa ya ƙarfafa masa gwiwa a wannan takara tasa.
Injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya ƙara da cewa “gaskiya na ji daɗi ƙwarai yadda al’ummomin waɗannan ƙananan hukumomin, inda muka shiga kowacce ƙaramar hukumar, suka fito ƙwansu da kwarkwatarsu, domin yi mana baici, wanda abinda na gani ya ƙara man ƙwarin gwiwa kan wannan takara da nake yi, sun nuna man ƙauna da soyayya kuma a kowacce ƙaramar hukumar 11. Maganar gaskiya na yi farin ciki matuƙar gaske, an nuna man karamci,”Inji Darma.
Ya bayyana manufofin sa na raya jihar Katsina da ƙasa baki idan aka bashi dama.
“Ƙwarewa da nayi ina siyasa da muƙamai da na riƙe a gwamnatin Katsina da kasa baki ɗaya yasa naga har da kiraye kiraye da al’umma ta ke yi na in fito takarar yasa naga bani da wata mafita illa in amsa kira da tabbacin zan iya bada tawa gudummawa wajen raya ƙasa.
