Ba zan taɓa cin amanar iyalan Buhari ba – Gwamna Raɗɗa

Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa a matsayinsa na wanda ya ci gajiyar alherin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ba zai taɓa cin amanar iyalan tsohon shugaban ba ta kowace hanya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar masu ruwa da tsaki na APC daga mazaɓar tarayya ta Daura, Mai’adua, da Sandamu, waɗanda suka ziyarce shi don gabatar da Yusuf Buhari, ɗan marigayi Muhammadu Buhari, a matsayin ɗan takara daga mazaɓar.

Gwamna Raɗɗa ya ba da labarin yadda ya ci gajiyar marigayin Shugaban tun 2015..

“Ba zan taɓa cin amanar iyalan Buhari ba. Na kasance mai cin gajiyar kyakkyawan sunarsa tun zamanin CPC har zuwa yau. Buhari ya rasu a halin yanzu Allah Ya jiƙansa. Saboda haka, ina yi wa Yusuf fatan alheri da kuma dukkan alheri a harkokin siyasa” in ji shi.

Ya bayyana cewa a yanayin dimokuraɗiyya, APC ba za ta hana kowa tsayawa takara ba saboda Yusuf Buhari yana cikin takarar, yana mai lura da cewa mahaifin Yusuf ya fafata tare da wasu da yawa kafin daga baya ya yi nasara, saboda haka, ‘kowa yana da ‘yancin yin takara.’

Gwamnan ya buƙaci Yusuf da ya gina wa kansa suna yayin da yake shiga siyasa.

Tun da farko a jawabinsa, Yusuf Buhari ya gode wa masu ruwa da tsaki daga mazaɓar tarayya kuma ya yi alƙawarin ba zai ba su kunya ba. Ya ce goyon bayan da yake samu daga mazaɓu ya kasance abin karfafa gwiwa kuma ya tabbatar musu da cewa zai tabbatar da amincewarsu ta hanyar biyan buƙatunsu.

Yusuf Buhari da masu ruwa da tsaki sun kuma ziyarci Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir Usman, a matsayin wani ɓangare na rangadinsa na neman albarka kafin zaɓen fidda gwani na APC da kuma babban zaɓen 2027.

By ukarofi