Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyyar adawa ta ADC a jihar Katsina ta zaɓi JaKada Muhammad Rimi matsayin shugaban jam’iyar bayan kammala zaɓen shugabannin jam’iyar gabanin zaɓen 2027.
Zaɓen da ya gudana a Munaj hotel ya sami halartar manyan ya’yan jam’iyar a matakin jiha da ƙasa da wakilai daga mazaɓu 361 daga jihar Katsina.
Da yake jawabi bayan kammala zaben tsohon shugaban jam’iyar ta jiha Lawal Ɓatagarawa ya bayyana mahimmancin haɗin kai da zaman lafiya tare da sanya jam’iyyar a gaba.
Shima jagoran adawa a jihar Katsina Mustapha Inuwa ya gargaɗi ya’yan jamiyar da su guji rikice rikicen cikin gida inda ya zargi wasu da aka ɗauki nauyi su wargaza jam’iyyar.
Yayi kira ga ya’yan jam’iyar da su zama masu ɗa’a da biyayya tare da maida hankali wajen ƙarfafa ƙarfin jami’ya.
Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Babangida Talau ya bayyana cewa zaɓen ya gudana ta hanyar sasanci bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki na jam’iyar.
Ya bayyana ce an samu saɓani gabannin sasanci amma daga baya aka sasanta tare da gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Sauran sabbin shugabannin sun haɗa Mansir Mu’azu a matsayin mataimakin shugaba da Mukhtar Adahama matsayin sakataren jam’iyar.
Sanata Babba Kaita wanda ya sa ido kan zaɓen ya ce aikin sa shine ya tabbatar da ingantaccen zaɓe, a cewar sa zaɓen ya gudana cikin gaskiya da nuna adalci wajen sasanci a tsakanin ‘yan takara.
Shugaban kwamitin zaɓen da Uwar jam’iyar ta tura Atiku Abubakar Sale ya tabbatar da sahihancin zaɓen.
