Da Ɗumi-Ɗumi: DSS ta gurfanar da El-Rufa’i kan naɗar hirar Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin sa da naɗar hirar wayar tarho ba bisa doka ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗauki matakin ne sakamakon zargin da ake yi wa El-Rufa’i na hannu a naɗar hirar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu.

Wannan tuhuma na ɗaya daga cikin waɗanda hukumar ta shigar akan sa tun a watan Fabrairu a ƙara mai lamba kamar haka FHC/ABJ/CR/99/2026, inda ake zargin tsohon da taka dokokin ayyukan da aka haramta a yanar gizo da kuma na dokar sadarwa ta 2003.

Ana tuhumar El-Rufa’i ne da laifuka biyar bayan an yi wa tuhumar gyara daga uku zuwa biyar, inda alƙalin kotun ta soke tsohuwar tuhumar tare da cigaba da sauraron sabuwar da aka gabatar mata.

El-Rufai dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, wanda hakan ya sanya lauyansa ya nemi a ba shi damar tattaunawa da wanda yake karewa, yana mai cewa al’amarin na hannun hukumomin tsaro daban-daban.

Sai dai alƙalin kotun ta ce ba ta ga ƙarin bayanin da aka ce an shigar ba, inda ta bukaci lauyan ya bi ka’idojin shigar da takardu yadda ya dace.

Da fari, El-Rufai ya bayyana a wata hira ta gidan talabijin cewa an saurari hirar wayar Ribaɗu, inda ya zargi gwamnati da sauraron hirar wayoyin jama’a ba tare da izini ba.

By Babaji