Tinubu ya amince da tallafin kamfanonin jiragen sama kan tsadar mai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta amince da wasu muhimman matakan tallafi domin rage wa kamfanonin jiragen sama raɗaɗin tsadar man jirgi (Jet A1), wanda ke barazana ga ci gaba da harkokin sufurin jiragen sama a Nijeriya.

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, bayan wani muhimmin taro da ya shafe sa’o’i ana gudanarwa tare da wakilan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, masu kamfanonin jiragen sama da kuma dillalan mai.

An gudanar da taron ne sakamakon ƙara tsanantar farashin man jirgi, wanda masu harkar sufurin jiragen sama suka bayyana a matsayin abin da ya gagari ɗauka, tare da yin barazanar dakatar da ayyuka idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.

Keyamo ya ce Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da rage wasu kudade da kamfanonin jiragen sama ke bin gwamnati, domin rage musu nauyin da ke kansu a halin yanzu.

A cewarsa, wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na gaggawa domin kare fannin sufurin jiragen sama daga durƙushewa, tare da tabbatar da cewa zirga-zirgar jirage ba ta tsaya ba.

“Shugaban ƙasa ya amince da rage wasu kudade da kamfanonin jiragen sama ke biya ga gwamnati domin ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin sauƙi,” inji Keyamo.

Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa a cikin kwanaki masu zuwa, shugaban ƙasa zai kafa wani kwamiti na musamman da zai duba tare da rage yawan haraji da caje-caje da ake ɗora wa tikitin jirage.

Ya ce matakin zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan kamfanonin jiragen sama da kuma fasinjoji, tare da ƙarfafa dorewar harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tashin gwauron zabi na farashin man Jet A1, wanda masu harkar jiragen sama suka bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke barazana ga ci gaba da ayyukansu da kuma daidaiton fannin sufurin jirage a Nijeriya.

Masana harkar sufurin jiragen sama na ganin cewa idan aka aiwatar da waɗannan matakai yadda ya kamata, za su taimaka matuƙa wajen rage matsin tattalin arziki da ke kan kamfanonin jiragen sama, da kuma kare fannin daga matsaloli a nan gaba.

By ukarofi