Tinubu ya amince da kaso 30 na sauƙaƙa bashi ga kamfanonin jiragen sama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ragin kaso 30 na bashi da kamfanonin jiragen sama suka riƙe wa hukumomin sufurin jiragen sama, a wani yunƙuri na rage matsin tattalin a gare su yakin farashin fetur ya yi tashin gwauron zaɓi.

Ministan sufurin jiragen sama da bunƙasa sararin samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana haka a wata takarda a juya Alhamis.

​Keyamo ya ce wannan ragi ya biyo bayan karɓar saƙon ne daga hannun Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa.

Matakin ya zo ne bayan korafe-korafen da kamfanonin jiragen sama suka yi kan tsadar man jiragen sama (Jet A1), wanda ya ƙaru matuƙa a ‘yan kwanakin nan.

A cewarsa, gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne domin hana yiwuwar dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a cikin kasar, bayan da wasu kamfanoni suka yi barazanar dakatar da aiki saboda tsadar mai da sauran kayan aiki.

Haka kuma, ana sa ran gwamnati za ta cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin daidaita farashin man jiragen sama da kuma rage wasu haraji da ke ƙara nauyi a kan kamfanonin, waɗanda ke haddasa musu tsaiko a lamuran gudanarwa.

By Babaji